Connect with us

Uncategorized

Dalilin da yasa ban ji Raguwa ba da mataki na ga Sayar da Bindigogi ba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Mai Suna Musa Mora wanda matakan tsaro suka kama da bindigogi

Matakan Tsaro sun kama wani mutum mai Suna Musa Mora wanda aka taras da shi da makamai daga garin Babana a Karkarar Borgu ta Niger.

An kama wannan mutumin mai shekara Arba’in da Biyar (45) ne da bindigogi guda shidda (6) da kuma bindiga  mai maharbi daya da ma’ajin harsasu guda uku.

An gane da cewa wannan mutumin da wani abokin aikin sa mai suna Babangida Rabiu daga Dangulu daga Zamfara State sun taba zuwa Kasar Benin domin sayan kayakin hari da dama.

Mora ya gaya wa Punch da cewa ya tsayo bindigogin ne daga Kasan Benin kuma yana sayar da shi ne ga duk mai bukatan tsaron kansa.

“ Ni kan saye bindigogi ne kuma in sayar ma mutane masu bukatar tsaro da kansu, Amma idan fa sun yi wani mugun aiki dashi, babu ruwa da wannan,” in fadin Mora.

Mora fada da cewa wannan sana’ar ya kai shekara shidda a cikinta kamin abokin sa ya hada hannu dashi, kuma sun sami kudi da dan dama ga wannan sana’ar sayar da bindigogi. Ya kuma nuna da cewa bai ji raguwa ba da wannan mataki nasa domin kuma a ciki ne yake rayuwa. kuma ba na kashe mutane da bindigogin”.

Mai yada Labari na wannan Jiha, mai suna Muhammad Abubakar, yace Musa ya tabbatas da wannan tuguma da aka yi masa.

“Yan Sanda ba zasu bada dama ba ga ajiyan makamai ba irin wannan in wannan Jihar kuma suna fadi ga kowa domin su rabu da irin wannan aiki da hali ko kuma mutum ya fada ga hukumci,” Inji shi Abubakar.

Yace ce an kai wannan mutum ko ga kotu.