Connect with us

Labaran Najeriya

Nnamdi Kanu yace ba a yi musanman Buhari ba amma an yi musayan sa da Jubril din Sudan

Published

on

at

advertisement

Nnamdi Kanu, Shugaban yan Biafra, ya tsayad da cewa an yi munsayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da wani da ake ce da shi ‘Jubril Aminu Alsudani’.

Wannan shugaba na IPOB ya bada muhimmai shida 6 don tsayar da fadin sa da cewa an munsaya Shugaba Muhammadu Buhari

Naija News na da sanin cewa Kanu ya fadi wannan ne a labarai da aka watsar daga Israila a ranar Sati da ta wuce, ya fada da cewa:

“Kwanaki da dan dama shugabancin Najeriya tayi kokarin da cewa ta tsananta ko kuma hana yaduwar wannan magana da cewa wannan mutumi da ke kai da kawo wa ko kuma shugabanci Najeriya ba Muhammadu Buhari ba ne sai dai Jubril daga Sudan”.

Baban cancatiyar misali da za a iya munsayar wani da wani shi ne da cewa ya zama dole wanda za a musanya yayi kama da wanda za a musanya shi.

da daman lokatai akan koyawa irin wannan mutumin yarda zai yi furci ko magana kamar wanda ake so a musanya shi.  wannan ya taba faruwa bisa ga labari, a sani ga wani mai suna Josef Stalin na defunct Soviet da kuma Adolf Hitler na Germany. akwai misalin wannan da dama, musanman a lokacin Yakin Duniya na biyu da Yakin Cacar baki.

Dubin wannan akayi munsayan Buhari da Jibril, sabo da yawan kamannin sa da Buhari. aka kuma yi masa tiyata ta roba domin ya karasa ga kamanin sa da Buhari, aka kuma koyar da shi yadda zai iya magana da aikata hali kamar Buhari.

Amma abin da ba a sani ba shine babu mutum biyu da zasu taba zama iri daya, ko yan’biyu ma da suke kamanni daya suna da dan banbanci. Haka kuma aka iya gane da cewa wannan mutumin da ke shuganci, ba Buhari ba ne.

Na daya, Buhari na da misalin shekara saba’in da bakwai (75) lokacin da ya hau mulki a shekara ta 2015. ya nuna da allamun shekarun sa, da kuma allamun tsufa da kuma rashin lafiyar jiki dake damun sa a wannan lokaci. dubin wannan Jibril na da misalin shekaru Hamsin (50), shekarun kuma sun nuna ga tsarin jikin sa har ga kamanin kunnuwan sa wanda ke da banbanci ga mutum biyu.

Na biyu, Buhari da tsufan sa ya na da sanko da yan farin sunma da ya rage a kan sa. abin manmaki ne da cewa wannan Mallam Jibril na da summar kai da dan dama bisa ga na Buhari. sa annan yana saye da fulla kullum wanda ya ki ya cire shi ko da ma an so haka.

Na Ukku, Ko da shi ke Buhari Bafillace ne kuma yana ji da fadin yaren Fulfude da kyau. Haka kuwa yakan yi magana da Hausa dakyau. Abin kulla ne da cewa wannan Jibril ba ya yin yaren Fulfude sai Hausa kawai. shi yasa yake yaren Hausa kawai a duk lokacin da ake bukatar sa da magana da yin yaren Fulfude.

Na Hudu, tun Watan Biyu shekara da ta wuce, Jibril yayi nisa da kansa da Iyalin Buhari, har ma ga Matan Buhari, Aisha da Yaron sa Yusuf. haka kuma Aisha ta yi nisa kuwa da shi. an kuwa nuna ga hoto yadda Yusuf ke ba Jibril hannu bayan dawo wan sa daga asibiti a Jameni don kula da lafiyar jikin sa.

Na biyar,  Buhari mutum ne mai tsawo sosai har ma tsawon sa yafi kamanin Sanata Saraki, amma abin yanzun nan shine Sanata Saraki da wadansu da Buhari yafi tsawo nuna da fiye shi da tsawo yanzun nan. Yaya haka ya faru? Lai Mohammed yace da cewa Buhari ka sanya dogayen takalma ne da, amma tun da ya fara rashin lafiya doktan sa ya bada shawara cewa ya bar sa irin wannan takalma, shi yasa ya nuna kamar ya rage tsawo bisa ga da.

Na Shida, tun lokacin da aka ce Buhari ya sami cikaken lafiya daga dawowar sa daga asibiti a London, ba ya kara komawa London ba don cin gaba da binciken lafiyar sa. wannan na iya faruwa kuwa? mutumin da yayi rashin lafiya har ga fuskar mutuwa ya koma sarai har bai koma da bin ciken lafiyar sa ba?

Ina tabbatar maku da cewa wannan mutumin ba Buhari ba ne amma Jibril wan da aka yi masa tiyata ta roba da kuma koya masa yadda zai yi magana ko tafiya iri ta Buhari.