Labaran Nishadi
Ba zani Manta da yan Shirin Fim, Mawaka da Yan Nanaye ba – Inji Atiku Abubakar
Alhaji Abubakar Atiku Yace ba za ya Manta da Yan Fim, Mawaka da Yana Nanaye ba
Alhaji Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, ya fada da cewa idan har nuna masa so kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019, zai tabbatar da ganin cewa bai manta da bangaren nishadi na Najeriya ba.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a wata takardar inda ya nuna aikace aikacen da zaya gudanas a Najeriya a tsawon shekaru shida daga 2019 zuwa 20125 indan har ya hau kan mulki a Najeriya. Yayi nuni zuwa ga matsaloli da ake samu a bangaren nishadantarwa, kuma yace zai magance su. Wasu daga cikin matsalolin da Atiku ya ambato na kamar haka; matsalar samun isassun kudade wajen gudanar da aikace aikacensu, satar fasaharsu, sayar da ayyukansu ba tare da izininsu ba, rashin sanin hanyoyin watsa kayansu a kasuwannin duniya, da kuma rashin samun tallafi, da sassaucin kudin wajen biyan haraji.
“Nayi alkawarin magance duk wadannan matsalolin” in ji Alhaji Atiku Abubakar.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya tabbatar da burinsa na sayar da kamfanin man fetir na Najeriya da matatun man fetir guda hudu na Najeriya gaba daya don samun isassun kudade a Najeriya. Kaakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Segun Sowunmi ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace idan har Atiku Abubakar ya ci nasara a zaben 2019, zai sayar da matatun man fetir gaba daya, yan Najeriya zai sayar ma wa.