Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Talata 11, Watan Shabiyu, a Shakara ta 2018

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata 11, ga Watan Shabiyu, 2018
1. Cin Hanci da Rashawa ta Kungiyar PDP a Shekara ta 2015 ya sa na sami cin nasara ga hawan mulki – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fadi da cewa Kungiyar APC ta ci nasara ne ga zaben Shekara ta 2015 saboda irin halin cin Hanci da Rashawa a shugabanci na PDP a wannan lokaci.

Shugaban kasa ya fadi wannan ne lokacin da yake bude wata kungiya ta binciken cin hanci da rashawa a Abuja.

2. EFCC ta ce karya ne, bamu kama yaron Atiku ba

Kungiya ta Binciken Kudi da Tattalin Arziki ta Kasa (EFCC) ta ce ba gaskiya bane da cewa sun kama yaron Alhaji Atiku Abubakar dan Takarar Shugaban kasa daga kungiyar PDP.

Mr Tony Orilade, Mai Rikon kwarya ta Kakakin EFCC, ya fadi wannan ne a ranar Litini a garin Abuja.

3. Dogara yace Rabon Kudi daga Gwamnatin Tarrayya shiri ne na siyar zabe ta Shekarar 2019 da ke gaba.

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon Yakubu Dogara, Ya haramta wannan mataki na rabon kudi ga jama’a da cewa wannan hali ce ta Cin Hanci da Rashawa. ganin cewa zabe ta 2019 ta kusanto.

Dogara ya fadi wannan ne ranar Litini, a lokacin da yake bada magana ga wata taro wanda Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokoki da Kungiyar INEC ta shirya.

4. Hadaddiyar Kungiya ta Krista mai suna ‘CAN’ na taron a rufe d Buhari da Atiku

Manyan yan takara guda biyu ta sama ta zaben Shugaban Kasa ta 2019 na Taro a rufe da Hadaddiyar Kungiya ta Krista (CAN) a Cibiyar Nazarin ta Krista a Abuja.

Rev. Samson Ayokunle, Shugaban Kungiya ta CAN, a fadin sa ga wani dan Jarida yace wannan taron muna yin shi ne don mun binciki Yan Takarar guda biyu don mu san shirin su ga wannan Kasa da kuma Krista idan kowane a cikin su ya sami hawa Kujerar Shugabanci.

5. EFCC sun kai hari ga gidan yaron Atiku Abubakar

Kungiyar EFCC sun binciki gidan da yaran Abubakar biyu ke zama a garin Abuja a karshen mako da ta wuce.

Wannan gidan na hade ne da wajen zaman wani tsohon Gwamna na Jihar Abia mai suna Chiemeka Orji.

6. Masu Tsayar da Man Fetur sun tsayar da yajin aiki, Gwamnatin Hadayya ta bada kwana biyar don ta biya tallafi na Mai.
Shugaban wannan Kungiya ya bada umuryi da cewa duk kowane dan kungiyar su yi yajin aiki su kuma kulle wajen aiki duka.

Olufemi Adewole, Sakatari na wannan kungiya ‘DAPPMAN ya fadi wannan ne daren Lahadi da ta wuce.

7. EFCC sun rike Doyin Okupe

Kungiya ta Binciken Kudi da Tattalin Arziki ta Kasa (EFCC) sun rike mai suna Doyin Okupe, wata ma aikata ce da ke kusa da Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

Wani dan Kungiyar PDP mai suna Kola Ologbondiyan ya bada wannan, fadin cewa wanna lokaci ne and hargitsin yan Kungiyar PDP.

8. Shugabanci ta Zargi PDP da yada karya labari

Garba Shehu, Babban Mataimakin Shugaban Kasa a Kafofin watsa labaru da yada labarai ya zargi PDP da cewa suna yada labarai da ba gaskiya ba.

Ya kara da cewa fadin su game da cewa an rufe aljihun ajiyar kudi ta Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP watau mai suna Peter Obi, da kuma zargin cewa EFCC sun Hari gidan yaran Atiku babban karya ne.

9. PDP su ki Kashamu a zaman Dan Takarar Gwamna na Jihar Ogun

Jam’iyyar PDP sun fada da cewa basu yadda ba da wannan Sanata na Gabas ta Ogun, watau Sanata Kashamu Buruji. da cewa zai zama masu kaya ga zabe mai zuwa kuma da dubin zai kawo tashin hankali da kungiyar.

Kola Ologbondiyan, Sakataren Watsa Labarun ta PDP, yace har yanzu wanda suka yadda da shi ya cigaba da wannan takara shine Ladi Adebutu a wannan jiha ta Ogun.

10. Ka bayyana makiyaya a matsayin ‘yan ta’adda – Bishop na Ikklisiyar Anglican ya gayawa Buhari

Bishop na Ikklisiyar yan Anglika ya gayawa Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya bayyana Makiyaya a zaman Yan’Ta’adda.

Ya fadi wannan ne a lokacin da yake magana game da irin yadda aka rasa rayuka da yawa akan harii na wa’enan Makiyaya a kasar na tamu.