Connect with us

Labaran Najeriya

Yadda na ci kujerar Shugabanci a shekara ta 2015–Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace kungiyar APC ta ci zaben shekara ta 2015 ne saboda yanayin da kasar mu ta lallace da chin hanci da rashawa a lokacin shugabanci na kungiyar PDP a wannana lokaci.

Shugaban kasa ya fadi wannan ne lokacin da yake bude wata kungiya ta binciken cin hanci da rashawa a Abuja.

Shugaban kasa ya iya nuna da cewa yanayin cin hanci da rashawa a kasar a wannan lokacin ya raunana kasar.

Shugaban Kasa Buhari ya ce gwamnatin na kokari ta ga cewa a kame duk wanda aka samu da wannan hali na cin hanci da rashawa a kuma hukumta shi, ya kara da cewa yana kokarin da cewa ya yi shugabanci na kwarai da kuma marasa cin hanci da rashawa.

“ A lokacin da muka hau mulki a Watan Biyar ta Shekara 2015, Yanayin cin hanci da rashawa a lokacin ya sa duk kokarin mu bai bayyana da nasara ba.

“Mun dauki matakai da dama tun watanni da yawa da suka wuce da ganin cewa mun tsayad da shugabanci ta gaskiya da rashin cin amana da kuma ganin cewa mun kame duk masu raunana kasar mu ta wurin son kansu bisa ga kasar.

“Cin nasara ga wannan ya zama babban aiki gare mu, duk da cewa an sami cigaba amma harwa yau cin hanci da rashawa na kokarin juyo mana.

Shugaban Kasa Buhari ya iya bada shawara da umurni ga shugabannai da cewa su tsayar da matakai na kwarai wanda zai iya hana ko kuma tsananta wa masu wannan hali ta cin hanci da rashawa.

Shugaban Kasa yace Najeriya ta wannan hanya, ta iya tsayar da matakai.

Yace wannan matakai na kamar; Bude Aljihun ajiya guda daya tak, Namba ta binciken gidan ajiyar kudi, Hadaddiyar kungiyar ta Gwamnati, Kungiyar Tsaro da tsayad da cin hanci da rashawa da de sauransu.

“Ga wannan matakai ne kawai zamu iya tsayad da wannan hali ta cin hanci da rashawa da kuma ganin cewa Kungiyar Tsaro ta Cin hanci da rashawa ta karfu”.