Connect with us

Uncategorized

Menene dalilin da ya sa kungiyar malaman kwalejojin fasaha ta shiga yajin aiki?

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

DALILIN DA YA JAWO YAJIN AIKIN DA MALAMAN KWALEJOJIN FASIHA SUKA SOMA?

Kungiyar malaman kwalejojin Fasaha a Najeriya wato ASUP ta bayyana dalilan da suka sa ta tsunduma cikin wani yajin aiki na sai illa masha Allahu.

ASUP ta bi sahun kungiyar malaman Jami’oi na Najeriya ASUU da suke ci gaba da yajin aiki fiye da wata daya.

Kungiyar malaman Kwalejojin na neman gwamnati ta biya wasu bukatunta ne guda goma sha daya.

Uwar kungiyar ce ta umurci ‘ya’yanta da su fara yajin-aikin na sai baba ta gani bayan shugabanninta sun kasa daidatawa da gwamnati.

Kungiyar ta yi zargin cewa an sha yin yarjejeniya da gwamnati amma ta kasa aiwartawa.

Shugaban kungiyar ta ASUP, Usman Yussuf Dutse ya shaida wa BBC cewa sun yi yajin aiki na barazana, amma gwamnati ta ce su dada ba ta lokaci kuma har lokcin ya wuce ba wani abu a kasa,

Ya ce bukatun da suke nema sun hada da samar da kayayyakin bincike a kwalejojin.

Gwamnati ta kafa kwamiti a 2014 da ya zagaye kwalejojin fasahar domin diba bukatun malaman. “Kwamitin ya bayar da rahoto amma har yanzu ba a aiwatar ba,” in ji shi.

Kungiyar ASUP ta ce duk da cewa dukkanin bukatun da ta gabatar suna da muhimmaci amma suna son ganin kokarin da gwamnati za ta iya yi da kuma bukatun da ta ke son a ba ta lokaci.

Shugaban kungiyar ASUP reshen Kano, Dakta Ahmad Zubairu Chedi ya shaida wa BBC cewa dole ce ta sanya su shiga yajin aiki, sakamakon gazawar gwamnati wajen aiwatar bukatunsu da suka jima suna bi.

Ya ce hakkokin sun hada wasu kudaden alawus da rashin biyan wasu malaman kwalejojin jihohi cikakken albashinsu da kuma batun aiwatar da shawarwarin da ke kunshe cikin wata kididdigar da aka yi a kan halin da kwalejojin Najeriyar ke ciki da hanyoyin inganta su.

Tuni dai yajin-aikin ya fara waragaza harkokin karatu inda dalibai suka shiga cikin wani hali na fargaba da rashin tabbas.

Naija News ta ruwaito Yan Fansho Jihar Neja chikin farin chi a yayin da aka fara biyar su kudin sallama

Kalla: Adamu Fasaha ya fitar da wata sabuwar bidio da suna MATAMBAYI