Uncategorized
Sabuwa: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta
Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau mai Nafisa Abdullahi ta bada karin haske game da matsayin Ali Nuhu a wajenta musamman ma dai a harkokin masana’antar.
Jarumar ta kara da cewa ta fito a fina-finai da dama da ta kiyasta da ‘sama da 50’, ta shaida wa majiyar BBC a lokacin da ta zanta da ita kai tsaye a dandalin sadarwar zamani na Facebook cewa, fitattcen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya wuce matsayin aboki a wajenta.
Karanta Kuma: Ba zan Manta da Yan Fim, Mawaka da Yana Nanaye ba – Alhaji Abubakar Atiku
“Yadda zan zauna na yi magana da sauran jarumai, ba zan iya yi da Ali Nuhu ba,” in ji Nafisa.
Ta ce Ali Nuhu ne sanadiyar zuwanta a Kannywwod.
Nafisa Abdullahi dake zaman daya daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fina-finan Kannywood ta kuma bayyana yadda ta soma shiga harkar fim bayan ta hadu da jarumi Ali Nuhu a shekarun baya a jihar Bauchi.
Naija News ta ruwaito Takaitaccen Bayani game da Fati Washa