Connect with us

Labaran Najeriya

Zan saka wa duk magoya na – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Buhari ya ce zai saka wa mutanen da suka goyi bayansa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce a wannan karon zai saka wa duk mutumin da ya goyi bayansa sannan ya yi aiki tukuru.

Ya bayyana haka ne ranar Laraba da almuru a wurin taron da kungiyar da ke goyon bayan siyasarsa, Buhari Support Organisation, ta shirya a Abuja.

Da alama shugaban ya yi wadannan kalamai ne saboda zargin da wasu da suka dade suna goyon bayansa suka yi cewa ya yi watsi da su bayan ya zama shugaban kasa a 2015.

Shugaba Buhari ya “watakila na bata ran wasu daga cikin mutane da kungiyoyi saboda bamu iya yi biya wa kowa bukatarsa ba. Ina so na tabbatar muku cewa a wannan karon za mu saka wa wadanda suka yi aiki tukuru sannan suka goyi bayanmu.”

Shugaban kasar ya kara da cewa taron da kungiyar ta hada ya tuna masa da irin gwagwarmayar da ya yi lokacin da yake neman shugabancin kasar.

A baya dai, wasu makusantan shugaban kasar – wadanda suka soma goyon bayansa tun da ya tsunduma harkokin siyasa – sun rika yin guna-guni kan abin da suka kira watsin da ya yi da su bayan ruwa ta sha.

Hakan ya sa da dama daga cikinsu komawa gefe suna da-na-sanin irin rawar da suka taka wajen ganin shugaban ya yi nasara a zaben 2015.

Sai dai wasu daga cikinsu sun soma matsawa kusa da gwamnati inda ake ganin su a fadar shugaban kasa ko da yake ba su da wasu mukamai.

A watan Fabrairu ne za a gudanar da babban zaben Najeriya inda Shugaba Buhari zai fafata da ‘yan takara fiye da 20.

Sai dai masu nazari kan harkokin siyasa na ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin sa da tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ke yin takara a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Naija News ta ruwaito Buhari na godewa Gwamnatin Swiss da yarda ta mayar da kudin da ta sata