Labaran Najeriya
2019 – Wasu Kungiyar Fulani sun ba wa Buhari goyon baya a Jihar Ekiti
Wata kungiyar Fulani a jihar Ekiti da suna, Gan Allah Fulani Association of Nigeria (GAFDAN) sun bayyana hadin kai da goyon bayan su ga Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019.
Kungiyar ta ce a shirye suke, kuma sun sanya matakan da za ta kawo ƙarshen duk wani tashin hankali a jihar.
Wannan kungiyar Gan Fulani ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta gabata cewa, “an sanya dukkan ayyukan da ake bukata don tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyayan jihar,” ya kara da cewa Fulani da ke a jihar sun bada gaskiya zamantakar lafiya a Jihar Ekiti da Najeriya ga ba daya.
Kungiyar GAFDAN ta zamantakewar al’umma na Fulani, a wata bayyani da shugaban kungiyar ya sanya hannu, watau Alhaji Issa Adamu, ya ce membobinsa na fahariya da ganin kasancewar zaman lafiya da al’umma duka a wannan Jihar da kuma ci gaban tattalin arziki na jihar da Nijeriya gaba daya.
Ya cigaba da cewa Fulanin dake a Jihar Ekiti na cikin zamantakewa ta lafiya, kuma suna tafiyar da harkokin kasuwancin su ba tare da wani kariya ba ko damuwa ba a yankin.
Sun bayyana amincewar su da gwamnatin Gwamna Kayode Fayemi, kuma sun yi alkawarin bada hadin kai da goyon bayan gwamnatin “kamar yadda ya haifar da ci gaba a jihar.”
Sun nuna murnan su ga Fayemi da mataimakinsa, Cif Bisi Egbeyemi jawabi, cewa: “Mun yi imani da cewa sabuwar gwamnatin za ta inganta rayuwar mutanen Ekiti gaba daya.
“Dawowarsa shine don inganta ayyukan Ekiti da ma’aikata a jihar. Muna da tabbacin cewa yana da guri ga abin da zai sa Ekiti ya bunkasa kuma ya canza. ”
A cikin bayyanin su, GAFDAN ta yi alfaharin amincewa da Shugaba Muhammadu Buhari, da cewa gwamnatinsa “ta yi nasara sosai.”
Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya don ganin cewa sun yi zabe don ci gaba da “nasarorin da gwamnatin Buhari ta yi a tsakanin 2015 zuwa 2018. Buhari dan siyasa ne mai ganuwa sosai da kuma babban janar soja mai ritaya wanda ya fahimci burin talakawan Najeriya.”
Naija News ta ruwaito Buhari tsoho ne amma ba wanda zai iya rinjayansa a zaben 2019