Connect with us

Labaran Najeriya

Ku ba ni yan Lokatai kadan don gane guri na -Buhari

Published

on

Ina rokon Yan Najeriya su bani lokaci

A yau ranar Litinin da Shugaba Muhammadu Buhari ke murnar ranar haihuwan sa na shekara 76 a garin Abuja, ya roki yan Najeriya su gane, su kuma fahimci manufarsa, a ba shi karin lokatai kadan da nan, a kuma ci gaba da taya shi da gwamnatin sa da addu’a.

Shugaban ya yi wannan kira ne gan yan Najeriya a gidan Majalisa a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a wurin bikin tunawa da ranar haihuwar sa ta shekaru 76.

Ya ce, “Za mu ci gaba da tunatar da ‘yan Nijeriya game da ayukan da muka iya yi, yanayin da muka iske kasar, abin da muka iya yi daga lokacin da muka hau mulki har zuwa yanzu tare da albarkatun da muka samu duka.

“Yan Nijeriya su ci gaba da yi mini addu’a, su kuma gane manufata, su ba ni lokaci kuma,” inji shi.

Ya ce yana nuna godiyan shi ga irin shiri da aka yi masa ga bikin ranar haihuwar shi na ganin shekara ta 76 a rayuwanshi.

“Ya kara da cewa, na gode da ganin hakan. Sun sanya lokaci mai yawa ga wannan shiri. Na gode da dukansu kwarai da gaske. “in ji shi.

 

Naija News ta ruwaito Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai saka wa duka wadanda suka goya mani baya