Connect with us

Labaran Nishadi

Zara ta aika wa Babanta sakon gaisuwa ta bikin ranar haihuwan sa shekara 76 a yau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Diyar Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Zara, a yau 17 ga watan Disamba, a Shekara ta 2018 ta rubutawa baban ta sakon gaisuwa ta musamman na murnan ganin tsohon ya kai ga shekaru 76 ga haifuwa.

Kyakkyawar mai haifuwa daya ta shiga filin nishadi ta Instagram dinta, don nuna murna da ganin tsohon ya kai ga shekaru 76 a yau Litini, 17 ga watan Disamba. tayi nuna wannan ne ta wurin aika da hoton tsohon da matarsa Aisha Buhari.

A sakon ta, Ta ce: “Albarka da farin ciki da shekaru mai yawa zuwa gareka da lafiya isashe. Allah ya albarkace ka ko ta ina”. a ranar haihuwar ka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, an haife shi ne 17 ga watan Disamba, 1942. Babban mai ritaya ne a cikin sojojin Najeriya kuma a baya ya zama shugaban kasa daga ranar 1 ga watan Disamba, 1983 zuwa 27 ga watan Agusta 1985, bayan ya karbi iko a juyin mulkin soja.

Barka da ranar haifuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari

 

Naija News ta ruwaito Buhari ya ce zai saka wa mutanen da suka goyi bayansa a zaben 2019 da ke a gaba