Jiha mai kyau ga Masu zuba Jari – in ji LOLO

Abubakar Sani Bello (LOLO) Gwamnan Jihar Neja ya bayyana matsayin Jihar sa a matsayin kasa mafi kyau ga masu zuba jari ganin irin kasancewar zaman lafiya da ake ciki a Jihar.

Gwamnan ya kara da cewa Jihar ta kasance Jiha mai kyau ga masu zuba jarurruka saboda yawancin al’umma da kayan jari dake a cikin ta.

Gwamnan ya bada wannan jawabi ne a yayin da yake gabatar wa na ganawa da jami’an hukumar kudi ta Afirka (AFC) kwanan nan, ya kuma yi alkawarin haɗin gwiwa tare da kungiyar a wuraren gyara hanyoyin, samar da wutar lantarki musamman ga yankunan karkara da kuma samar da ruwa.

Sanarwar daga Kwamishinan Bayanai, Alhaji Danjuma Salau ya bayyana cewa Bello ya fada wa jagorancin AFC cewa samun kudi da ake bukata don tallafawa ayyukan shi ne ya zama da babban matsala da muke fuskanta a jihohi da gwamnatin tarayya gaba daya. saboda haka ya kamata a hada gwiwa tare da manyan matallafan kasa daga waje.

Gwamnan ya ce a fadin sa, cewa duk da irin gurin sa na ganin a samar da ayuka na yaduwar kasa a Jihar Neja, samun kudin yin haka ya zama da matsala.

Naija News ta ruwaito Yan Fansho na cikin murmushi da Dariya a yayin da aka fara biyan su kudin sallama a Jihar Neja.

“A matsayinka jiha, muna da matukar tasiri kuma munyi imani akan cancantar ayyuka,” in ji shi.

Ya yi nadama da cewa ba a zuba jari da dama ba ga nazarin ayyukan albarkatun ma’adinai kamar yadda aka zuba wa bangaren man fetur da gas. Dalilin da ya sa gwamnatin ta kafa wata Matafiyar musamman watau (Zuma Mineral Development Corporation), don gudanar da bincike kan man fetur gas a jihar.

Bello ya shaida wa jami’an cewa, manyan ayuka dake da muhimin ga Jihar a halin yanzu itace hanyar Minna zuwa bida Bida da kuma Minna zuwa Tegina sabili da haka tana bukatar tallafawa daga matallafa ta kasashe.

A cikin bayyanin sa, Babban shugaban Jami’in AFC, Mr Samaila Zubairu ya ce Jam’iyyan na a shirye don hada hannu ga taimakawa ga ayyukar Jihar, da cewa Jam’iyyan zasu yi muhawara da jami’an gwamnati a kan al’amarin.

Karanta kumaKa koma Daura ka huta – PDP sun gayawa Buhari