Connect with us

Labaran Najeriya

Zan Sanya Matashi Minista har kasa da shekara 30 a mulki na – inji Atiku

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP yace zai Sanya Matasa har kasa da Shekara 30 a mulki idan a zabe shi

Atiku Abubakar, ya yi alkawarin bawa matasan Najeriya dama mulki a gwamnatinsa idan aka zabe shi a zaben shekarar 2019.

Ya yi alkawarin bayar da kashi 40 cikin 100 na rukunin gwamnati ga matasa, kuma ya sanya minista mai shekara 30 ko kasa da haka.

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya yi wannan alƙawari ne a wani taro na ganawa da matasa a jiya a Birnin Legas.

“Na yi alkawarin cewa kashi 40 cikin 100 na gwamnati na zai kasance matashi ne. Bari in tabbatar muku da cewa wa’adi ne kuma ba zan karya shi ba. Shugaban Ministar Matasa na zai kasance kasa da shekaru 30.

“Shugaba Buhari yayi furci da cewa tattalin arziki kasar mu na cikin mummunar siffa a karkashin jagorancin sa, wannan na a bayyane kuma a fili da cewa shugaban kasar bai da wani matakin mahinmanci da yadda za a gyara tattalin arzikin kasan nan. Babu wani masanin tattalin arziki daya cikin mulkinsa kuma shine dalilin da yasa muke cikin wannan hali da mu ciki.

“Na san yadda ake gyara tattalin arziki da ya samu raguwa. Na san yadda ake kirkiro aiki, kuma na san yadda zan karfafa matasa. Wannan shi ne dalilin da ya sa nake a nan yau – don ba da fata da kuma tabbatas maku Matasa da cewa a hade za mu iya samun gyara Najeriya, “inji shi.

 

Naija News ta ruwaito Alhaji Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, ya ce idan har aka nuna masa so kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019, zai tabbatar da ganin cewa bai manta da bangaren nishadi na Najeriya ba.