Connect with us

Labaran Najeriya

Najeriya ta bukaci jagoranci daga yan tsarar zamani ta 21 – Kingsley Moghalu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takarar Jam’iyyar Progressive Party (YPP) Kingsley Moghalu a yau Laraba, 19 ga watan Disamba 2018, ya bayyana cewa, Najeriya ta bukaci jagoranci daga yan tsarar zamani ta 21 don ci gaba da tsira daga matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu.

Moghalu ya bada wanna bayyani ne a wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas a wata zaman Sakawa ta 2018 (The Future Awards Africa) da ya sami halarta.

Ya ce: “Ina cikin tseren kujerar shugaban kasa don cin nasara, kuma da yardar Allah, zan zama shugaban kasa na Najeriya a shekara ta 2019; dalili kuwa shine jam’iyya ta shirya na a shirye don zamar da canji.

“‘Yan Nijeriya na bukatar sabuwar tsari; suna bukatar shugabanni masu hangen nesa da zasu iya tasiri ga rayukan al’umma. Kasar na bukatar jagoranci daga yan tsarar zamani ta 21 don ci gaba da tsira daga matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu.

“A matsayi na na dan takarar shugaban kasa da kuma tsohon mataimakin gwamna na Babban Bankin, ina a shirye da tsarfafen ilimi da hangen nesa da ake bukata ga shugaban Najeriya.

“Ina da kwarewa sosai da Ƙungiyar Majalisar Dinkin Duniya” (UN) da kuma kafa al’ummomi kamar Ruwanda, Croatia, Cambodia da sauransu. Ina a shirye da kwarewa na kwarai da gaske don jagoranci kasar. ”

Naija News ta ruwaito  Atiku Abubakar, ya yi alkawarin bawa matasan Najeriya dama mulki a gwamnatinsa idan aka zabe shi a zaben shekarar 2019. Ya yi alkawarin bayar da kashi 40 cikin 100 na rukunin gwamnati ga matasa, kuma ya sanya minista mai shekara 30 ko kasa da haka.

Moghalu ya bayyana cewa zuba jarurruka ga harkokin kasuwancin matasa ne kawai zai haifar da wadataccen tattalin arziki a kasar, ya kara da cewa zuba jarurruka ga mata ba zama isasshe ba.

Dan takarar ya ce: “Muna buƙatar zuba jari ga matasan kasar; Abin da ya sa kenan nake gabatar tsari wadatacciya da zai bunkasa kuma mayar da hankali ga matasa, ganin cewa matasa nada tsari kashi 70 cikin 100 na yawan jama’ar kasar.

“Tsarin kwarewa da karuwar ilimi ga koyan ayuka da ke cikin shiri na zai yadu ga yankuna 774 da muke da su a Najeriya duka in matasa zasu koyi ayuka karin jari.

Karanta kuma: Ka nemi wani asali amma bani ba ne sanadiyar kasawar ka ba a mulki, Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya gayawa Shugaba Buhari