Labaran Najeriya
Sabuwa: Ana tsuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari a yayin da yake bada Kasafin kudi na 2019
Abin takaici, ana ma Shugaba Muhammadu Buhari tsuwa a yayin da yake bada kasafin kudi na shekara ta 2019.
Naija News ta ruwaito Jam’iyyar PDP sun shawarci Buhari ya koma gidan sa a Daura yaje ya huta. sun fadi wannan ne wurin amsa wa rokon Shugaba Muhammadu Buhari inda yace yan Najeriya su bashi lokaci kadan. sun ce ba za a ba da shugabancin kasar nan ba ga mutumin da kullum a na neman ya huta, ya kuma yi barci dakyau.
Wannan kasafin kudi ne na shekara ta 2019, wanda aka sanar kwanakin baya da suka wuce, cewa a yau Laraba 19, ga Watan Disamba, a Shekara ta 2018 shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bada Kasafin kudi na shekarar 2019.
Kingin labarai zasu biyo baya………………
Karanta kuma: PDP sun sha kunya a yayin da Buhari bai Mutu ba a Landan – Lai Mohammed