Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: Wasu yan hari sun harbe Tsohon ofisan tsaro, Alex Badeh har ga mutuwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An Harbe Tsohon Babban Jami’in Tsaro, Alex Badeh

Abin kaito, Sojojin sama ta Najeriya sun sanar da mutuwar tsohon babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, mai suna, Air Chief Marshal, Alex Badeh (retd.).

A cewar mai magana da yawun rundunar Sojojin sama, Air Commodore Ibikunle Daramola, Dan haifuwar Jihar Adamawa mai suna Badeh ya mutu a ranar 18 ga watan Disamban, shekara 2018 sakamakon harbi da wasu yan hari suka yi masa a yayin da yake dawo daga gonarsa daga hanyar Abuja-Lafia.

Sanarwar ta zo ne kamar haka:

“Ina da bakin ciki da gaske in sanar maku da mummunar mutuwar Tsohon Babban Jami’in Tsaro, Air Chief Marshal Alex Badeh, wanda ya mutu a yau, ranar 18 ga watan Disamba 2018, daga raunin harbi da wasu yan hari suka yi masa cikin motarsa ​​yayin da yake dawowa daga gona a hanyar Abuja-Keffi. ”

“A madadin jami’an tsaro, ‘Maza da mata na rundunar sojojin sama ta Najeriya, Babban Jami’in Air Staff, Air Marshal Abubakar, muna nuna bakin cikin mu da wannan mumunar abu da ya faru da tsohon hafsan hafsoshin tsaro ga iyalan sa. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya sa ya huta lafiya.

Har zuwa lokacin mutuwarsa, Tsohon Shugaban tsaron na da tsayuwar ganawa a kotu don zargin aikata laifuffukan satan kudi da kimanin Naira biliyan uku da dari tara (N3.9B) a lokacin da yake shugabancin.

Bari ransa ya huta lafiya, amin.

Naija News ta ruwaito Ku gujewa Halaye da zai iya haifar da tashin hankali –  inji IGP Idris