Connect with us

Uncategorized

Yau ne ranar tunawa da haifuwar Bukola Saraki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shahararren dan siyasar Najeriya mai suna Bukola Saraki na bikin tunawa da ranar haifuwar sa a yau.

Shugaban Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki wanda aka haifa a  ranar 19 ga watan Disamba, Shekara ta 1962, na murnar tunawa da ranar haifuwar sa a yau.

Babban Bukola Saraki mai suna Olusola Saraki ya zama daya ne daga cikin Sanatocin Najeriya na shekarun baya, daga Shekara ta  1979 har zuwa 1983. Tsohuwar sa kuma mai suna Florence Morenike Saraki ta tabbatas cewa Sanatan, Saraki ya samu isasshen Ilimi na kwarai da gaske.

Bukola Saraki ya hau kujerar Shugaban Sanatocin Najeriya ne tun Shekara ta 2015. Zaman sa na dan Jam’iyyar Demokradiyya (PDP), yayi takarar Gwamnan Jihar Kwara a shekara ta 2003 ya kuma yi mulki har tsawon shekaru takwas (8) daga 2003 har zuwa shekara ta 2011.

Ya kuma shiga Sanata shekaru bakwai 7 da suka shige a Jam’iyyar PDP, ya koma takara kuma shekara ta 2015 a karkashin Jam’iyyar APC.

Dan siyasar a wannan shekaran ya komawa tsohon Jam’iyyar sa PDP.

Naija News na maka Barka da ranar haifuwa! Shugaba Saraki

Karanta kuma: Diyar Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Zara, a ranar 17 ga watan Disamba, a Shekara ta 2018 ta rubutawa baban ta sakon gaisuwa ta musamman na murnan ganin tsohon ya kai ga shekaru 76 ga haifuwa