Connect with us

Uncategorized

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an Sojojin Najeriya sun kame wasu yan Mata biyu da suka yi kokarin shiga yankin Sojojin don kai masu hari

Wasu yan mata biyu da ake tugumar su da zaman yan Boko Haram su fada hannun Sojojin Najeriya. Rahoto ta bayas daga bakin wani Jami’in tsaro na NSDCC mai suna Ibrahim cewa an kame yan matan ne biyu a daren Laraba 19, ga watan Disamba 2018, shiyoyin karfe tara 9 na dare a yankin Konduga ta Jihar Borno.

Bayan an kame su an iya gane da cewa guda cikin yan matan mai suna Fatima Muhammed Kabir a na sanye da rigan bama-bamai a jikin ta. an kame ta ne da abokiyar ta mai suna Amina Salihu a wata gareji motoci a babbar hanyan Borno. sun bayyana cewa wannan shiri ne na kai hari a yankin Maiduguri.

Naija News ta ruwaito Wasu yan hari sun kai farmaki da har sun kashe mutane 14, sun kuma yiwa mutane 17 rauni a daren Lahadi da ta gabata, a wata kauye, mai suna Ungwan Paa-Gwandara a yankin Jema’a na Jihar Kaduna.

A bayyanin shi Ibrahim, ya ce wasu yan kungiyar Boko Haram din da kimanin mutane arba’in 40 su tabbatar da cewa su fita, kuma sun musunci kungiyar ta’addan nan, kuma sun bayar da kayakin harin su ga jami’an tsaro.

“Mun musunci kungiyar ta’adda ta boko haram, kuma a halin yanzu muna sallah so biyar a rana fiye da yadda muke yi a cikin jejin sambisa” in ji ‘yan ta’addan da suka tuba.

Karanta kuma Jam’iyyar PDP a Jihar Benue sun bayyana bacin ran su game da matakin da gwamnatin tarayya ta ki ta yi a kan zargin da ake yi wa shugabannin miyetti da laifin kisan gillar da aka yi a jihar.