Connect with us

Labaran Najeriya

So ta gaske Buhari ke da shi ga kasar Najeriya – Yemi Osibanjo

Published

on

A kashin gaskiya so ta kwarai Shugaba Muhammadu Buhari ke da shi ga yan Najeriya gaba daya

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo ya bayyana Shugaban kasar a matsayin mutum mai kyakyawan hali da kuma nufi mai kyau ga kasar. kuma ya kasance shugaba dake da gurbi mai kyau kwarai da gaske.

Osinbajo, a ranar murnar tunawa da haihuwar shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da yake wata ganawa a can Austria da wata kungiya ta Africa da Turai. ya aika ta hilin nishadin twitter don nuna murnan sa da gaisuwa ta musanman ga shugaban.

Ya rubuta kamar haka; “Zuwa ga jarumin mutumi da ke da gurbi ta kwarai da kuma nuna jaruntan sa wurin gwagwarmaya da cigaban kasar Najeriya”.

Ya tura wannan sakon da wata hoto kamar wannan

Naija News ta ruwaito Diyar Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Zara, a yau 17 ga watan Disamba, a Shekara ta 2018 ta rubutawa baban ta sakon gaisuwa ta musamman na murnan ganin tsohon ya kai ga shekaru 76 ga haifuwa.