Connect with us

Uncategorized

Wata Rashi: Mutane Uku sun kone kurmus da wuta a wata hasari a Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Laraba da ta gabata, wasu mutane uku sun kone kurmus da wuta a sanadiyar wata hatsarin mota da ta faru a wata Gidan mai fetur na yankin Okene, a Jihar Kogi. Yan Kula da Lafiyar Tafiyar da Tuki (FRSC) ne suka bayyar da wannan.

Wani Shugaban Yan Kungiyar FRSC na yankin Okene, Adelaja Ogungbemi ya bayyana wannan ne a ganawar sa da manema labarai cewa wasu mutane da dama sun sami raunuka da gaske. ya kara da cewa motoci bakwai suka kone kurmus ga wannan hatsarin.

Wannan hatsarin ya faru ne shiyoyin karfe 11:16 na maraice a ranar Talata 18, Disamba 2018 a yayin da wata Babbar mota ta rasa birkin ta, taf gaba daya ta haro gidan man fetur sai kwaram ga wasu motoci da ke awurin. in ji Ogungbemi.

Ya ce, taimakon yan Kungiyan sa da hadin gwiwa mutanen da ke a wurin hatsarin ne ya sa hatsarin bai yi mumuna da yawa ba, da an yi wata babbar rashi da mumunar ci da wuta.

Gwagwarmayan rage wani ci da wuta na hatsarin ya ci gaba ne har zuwa karfe goma 10 na safiyar Laraba, An gyagyaran hanyar dan ganin cewa motoci da zasu biyo daga baya sun sami hanyar bi. in ji shi.

Sami cikakkun labarai na Hausa a Naija News Hausa