Connect with us

Uncategorized

Atiku zai raba Najeriya biyu idan har ya hau mulki – Alhaji Garus Gololo

Published

on

Idan har dan takar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku ya hau mulki a Najeriya, zai raba kasar biyu

Babban Shugaban kungiyar Miyetti Allah a Jihar Benue, Alhaji Garus Gololo ya bayyana ce wa idan har ‘yan Najeriya suka goyawa Atiku baya har ya hau ga shugabanci, to na tabbata zai raba kasar biyu.

Gololo ya fadi wannan ne ganin irin kalmar da kakakin yada yawun Atiku,  Phrank Shuaibu ya furda a wata ganawa da su ka yi a ranar Alhamis 20, ga watan Disamba 2018.

furcin na kamar haka; “za a yi kashe-kashe da yawa daga makiyaya idan har Muhammadu Buhari ya ci zaben shekara ta 2019”. ya bayyana wannan ne ga yan jaridun Punch.

Kwanakin baya Naija News ta ba da labari cewa Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, watau ƙungiyar zamantakewa da al’adu ta Fulani, sun fada da cewa sun kusa su nuna zabin su tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Dan Adawan sa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa watau Atiku Abubakar. Babban Shugaba na wannan Kungiya, watau Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, da Sakatare na kungiyar mai suna, Engr. Saleh Alhassan ya fadi wannan ne a ranar Jiya a Abuja a wata taron labarai.

Gololo ya ce “Atiku ya bani kunya kwarai da gaske, saboda ya riga ya raba Nijeriya tun ma bai ci zabe ba”.

Buhari ba shi da wani hurda da makiyayan, shi dan Najeriya ne, kuma mutanen Nijeriya ne suka sanya shi a mulki kuma ina mai bangaskiya cewa za su sake zaben shi a zaben shekara ta 2019.

Bai kamata yan Najeriya su nuna wa Atiku kuluwa ba da ganin irin mutumin da dan takarar yake.

Ya ce Fulani yan ta’adda bane kuma ba masu kashe rayuka bane kuma shugaba Muhammadu Buhari bai da wani hurda da Makiyayan. ya kara da cewa yan Najeriya da suka zabi Buhari a shekarar 2015 su zasu kara zaben sa a zaben 2019.

Ya karasa da cewa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar zar yanzu basu bada kulawa mai kyau ga kungiyar tasu ba ganin cewa dukansu Fulani ne.

Karanta kuma Yan PDP sun ce, Shugabannin Miyetti Allah ke da alhakin kashe-kashe a Jihar Benue