Labaran Najeriya
Baku fi karfin Doka ba, Buhari ya gayawa Jami’an tsaron Yan Sanda
Kuma baku fi gaban hukunci ba, Buhari ya fada wa Jami’an tsaron Yan Sandan Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari a wata gabatarwa da ya bayar ta wurin babban magatakardan sa, Garba Shehu a ranar Alhamis a wajen taron fitar da tsarin fasalin farko na wadanda suka kammala makarantar ‘yan sanda, Wudil, a Jihar Kano. Ya ce, Dole ne ‘Yan sandan su guje wa halayen da ba ta kwarai ba a yayin da doka ba zata yadda da wannan ba.
Bayanin na kamar haka;
“Rashin bin doka kamar, tsare tsare ba bisa ka’ida ba, kashe-kashen kisan kai, azabtarwa da kuma cin zarafi na ‘yancin ɗan Adam da sauran laifuka da bai dace ba, dole ne Yan sanda su guje wa irin wadanan halaye a kowane lokaci.
“Dole ne mu bi doka ta ganin cewa mun bi da al’umma dadai yadda ya kamata, idan har yan sanda zasu bukaci samar da ayukan tsaro yadda ya dace, to dole ne hada hannu da jama’ar gari. idan kuwa ba a yi wannan ba, samar da tsaro ga mutane zai zama da wuya a yayin da ba zaku iya hurda da al’umma ba”. inji Buhari.
Ya kuma yi anfani da wannan damma don shawartar su ce wa, Yan sanda su guje wa halin cin hanci da rashawa.
“Dadai ne in umurce ku ga wannan” inji Shugaba Buhari.
Naija News ta ruwaito da cewa wasu mazauna Jihar Nasarawa sun shaidawa Amnesty International (AI) da cewa ‘Yan sanda da aka aika a yankin don magance matsalar makiyaya sun bukace su da biyar kudi mai kimanin naira Dubu dari da hamsin (N150,000).
Kada ku ga kanku kamar kun fi karfin doka ta kama ku. ku guje wa duk wata hali da bai dace ba. bari albashin ku ya ishe ku ga duk kowace harka kuke da ita. “Ba a dade ba da Gwamnati ta kara wa albashin ku” don ganin cewa kun gudanar da ayukan ku yadda ya dace.
“Bari kuma in tunarsheku cewa wannan Gwamnatin ba za ta yadda da kowace irin halin cin hanci da rashawa ba. Cin hanci da rashawa ya sa kasar ke cikin halin da muke ciki a yau. idan ko har muna muradin mayar da kasan mu ga yadda ya dace, dole ne mu gujewa cin hanci da rashawa a kowace hanya.
”Ina a sane da cewa kun aika da sabbin yan sanda ofisoshi fiye da 2000, harma da Yan sandan rufe ido a Arewacin kasar don fada da yan ta’addan Boko Haram da goyawa Jami’an Sojojin Najeriya baya ga wannan fada”.
Wannan babban abu ce kuma na yaba maku da wannan nasara. inji Shugaban Kasar.
Karanta Kuma Ku guje wa halayen da za su iya haifar da tashin hankali Inspekta janaral Yan sandan, IGP Ibrahim Idris, ya yi kira ga hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro kasar da ‘yan siyasa, kafin zaben 2019 ta gabato.