Connect with us

Uncategorized

Boko Haram – An kame wani Shugaban yan Boko Haram mai suna Abdulmalik Umar

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

An kame wani mai suna Umar wanda  ‘Yan Sanda suka zarge shi a matsayin babban kwamandan Boko Haram a jiya a garin Legas

Abdulmalik Umar, wani  shahararen shugaban Yan Boko Haram da ake zargin sa da alhakin mutuwar mutane fiye da 200 ya shiga hannun yan sanda jiya a garin Legas.

IG na Yan Sanda da dakarunsa sun kame dan shekaru 39 din ne a shiyan Mowe, a Jihar Legas gidan wata Ma’aikatan asibiti wada ke kula masa da raunin alsasan harbin bindiga da ya ke da ita sanadiyar wata ganawa wuta da shi da Yan sanda suka hade a birnin Abuja kwanaki kadan da suka wuce.

Rahotanni ta bayar cewa wani mutumin ne ya yi sanadiyar tashin bama bamai da aka yi a Nyanya da Kuje a Abuja a shekarar 2015, da kuma wasu fashin bankuna da aka yi a Jihar Ondo, Edo da sauran jihohin. Umar ya gudu zuwa garin Legas makonni uku da ta wuce daga garin Abuja a sanadiyar ganin an kame wasu yan kungiyar.

Wata majiyar ‘yan sanda, wadda ta tabbatar da kame Umar ta bayyana cewa an kame likitan, wanda aka gane da cewa Yar’uwar Umar ce hade da mijinta da mijinta don taimakawa Umar da aikata mugayen hali.

An bayyana cewa, shugaban IRT, Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda (DCP), da kuma mutanensa sun shiga neman Umar tun shigar sa birnin Legas makonnai uku da ta gabata.

An gano mabuyan sa ne shiyoyin karfe biyu 2pm a ranar Alhamis 20, ga Watan Disamba, 2018.

“Umar na da ido ɗaya ne kuma yana da alhakin kashe mutane fiye da 200. Mun kame mutane hudu daga cikin mambobinsa a makonni uku da suka wuce a birnin Abuja, kuma mun gano bindigar AK47 guda hudu da suka kwace daga hannun ‘yan sanda da suka kashe a Gwagwalada”. in ji Yan Sanda.

“Ya tsere ne da raunukan bindigogi ya kuma gudu zuwa birnin Legas. Mun shiga nemar kama shi tun daga lokacin. a she ya tafi gidan ‘yar’uwarsa a Mowe don ya ɓoye. ‘Yar’uwar ce ke kula wa da rauninsa. Mun kame ta da mijinta kuma dalilin cewa su goyi bayansa da aikata mugayen hali irin wannan”. in ji Yan Sanda.

“Yan Sanda yu kara da cewa shi ne ya shirya fashe gidan jaru da ya auku a Jihar Neja a farkon shekaran nan, a inda ya rasa idon sa guda, ya kuma guje da yan yari kimanin 100”.

Mai yada yawun Yan sanda Jimoh Moshood, Mataimakin Kwamishanan Yan Sandan ya ce lallai gaskiya ne mun kame shi kuma za mu kashi gaban hukuma nan kadan.

Naija News ta ruwaito Jami’an Sojojin Najeriya sun kame wasu yan Mata biyu, yan Kungiyar Boko Haram da suka yi kokarin shiga yankin Sojojin don kai masu hari.