Connect with us

Uncategorized

Haram: Kungiyar HISBA ta Jihar Kano ta kame Yan mata 11 da shirin Auren Jintsi daya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Yan Kungiyar HISBA a Jihar Kano sun kama wasu ‘Yan Mata Goma sha daya 11 da zargin shirin yin aure na jinsi daya, watau Mace-da-Mace.

Wannan Kungiyar Shari’a ta Musulunci, watau HISBAH ta yi kamun ‘yan matan ne a ranar Litini da ya gabata. an kame yan matan ne a yayin da suke ganawa ta karshe domin shirin wannan aure na Jinsi daya.

“Babbar Daraktan ‘yan Hisbah, Abba Sufi ya ce bada cewa mutanenmu ne suka ji wannan shiri auren suka kuma yi kokarin halarta a wajen shirin, inda suka kame ‘yan mata goma sha daya 11 har ma da miji da mata na jinsi daya da ake shirin auratas da su”. in ji Sufi.

“Da zarar an mun kammala bincike, zamu bada su ga shari’a. “Ba za mu iya bude idanun mu ba ganin irin wannan mumunar halin kunya da haram na abkuwa a cikin al’ummar yankin mu ba.

Dokar Musulunci da dokar kasar Najeriya ta haramta jima’i tsakanin jintsi daya. in ji Sufi.
‘Yan matan da ake zargin su da aikata wannan shirin sun yi musun cewa ba gaskiya bane wannan zargin.

Cewa sun shirya taron ne don bikin ganawa da daya daga cikinsu a matsayin mataimakin shugaban kulob din na su, in ji rahoto daga bakin wani dan Hisbah.
Kungiyar HISBA ta ce wannan shi ne kamu na biyu birnin. shekara ta 2007 mun kama wasu ‘yan mata biyar daga Jihar don gudanar da auren mace-da-mace a wata ma shiryar wasan su.

Haka kuwa a Watan Janairu a shekara ta 2015, Kungiyar HISBAH ta kame wasu ‘yan Maza guda goma sha biyu a yankin Jihar Kano da shirin yin wannan aure ta jinsi daya, watau da na miji-da na miji dan uwarsa.

Naija News na da sanin cewa a shekara ta 2014, dokar kasar Najeriya ta bayyana cewa auren jintsi daya ya haramta. da cewa duk wanda aka kama da irin wanna shiri, za a hukumta shi ko ita. kuma za a jefa shi jaru na tsawon shekaru 14.

Karanta kuma Surukin Shugaba Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi ya nuna murna sa ga matarsa, Zahra Buhari na ganin ranar tunawa da haihuwan ta na shekaru 24.