Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Jumma’a 21, ga Watan Shabiyu, a Shakara ta 2018

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 21 ga Watan Shabiyu, 2018

1. Dakatar da shugaban kwamitin bincike, Okoi Obono-Obla- Yan Majalisa su gayawa Buhari

Yan Majalisar wakilai sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da, SPIP, Okoi Obono-Obla don kadamar da takardun da ba ta kwarai ba da kuma aikatar da cin hanci da rashawa.

Yayinda Majalisar ta bukaci shugaban kasa ya dakatar da kwamitin da Obla ya jagoranta, sun kuma nemi a yi amfani da dokar dokoki ta, CCB, don aiwatar da wannan yaki da halin cin hanci da rashawa.

2. Yan sanda sun kame wani babban kwamandan Boko Haram

‘Jami’an tsaron Yan sandan Najeriya sun kame wani babban jagoran kungiyar Boko Haram mai suna Abdulmalik Umar, wanda ake zargin sa da jagorancin fashewan bama-bamai da suka fashe a Kuje da Nyanya a birnin Abuja a shekara ta 2015.

Rahoto ta bayyar cewa dakarun IGP na Yan Sanda ne suka jagoranci wannan kamun a ranar Alhamis.

3. Jam’iyyar APC ta ce Ishola Balogun-Fulani ya saura a dakace

Shugaban Jam’iyyar APC ya ce ya yanke shawarar da kungiyar ta yi game da dakatar Ishola Balogun Fulani ya tsayu har yanzu a jagoranci a Jihar Kwara.

Jam’iyyar ta bayyana wannan ne ga wata sanarwa da Sakataren yada labaran Jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu ya bayar, a kan yanke shari’ar da kotun koli na Ilorin tayi akan dakatar da Abdulrahman Abdulrazaq a matsayin dan takara na APC a Jihar Kwaraa ranar Laraba da ta gabata.

4. Majalisar Dattijai ta sanya Bolaji Owasanoye a matsayin shugaban hukumar ICPC

Majalisar a ranar Alhamis 20, ga Watan Disamba 2018, ta sanya Farfesa Bolaji Owasanoye a matsayin Shugaban Hukumar Kungiyar ICPC.

Majalisar kuma ta bayyana karbar wasu mutane takwas 8 a matsayin mambobin kungiyar ICPC.

5. Shugaba Buhari ya gudanar da bude wata sabuwar kofar shiga filin jirgin sama a Abuja

A ranar Alhamis da ta gabata, Shugaban kasar Muhammadu Buhari gabatar da bude a sabuwar kofa a fillin jirgin Nnamdi Azikwe ta birnin Abuja.

Da shugaban ke bada jawabin sa a taron, ya ce Nijeriya zata cigaba da ganin an samar da gudanarwa ta kwarai domin cimma lafiyayen ma’aikata, inda ma tafiya zasu sami isashen gudanaswa ga tafiya da kuma saukarwa ko karbar kayansu.

6. Majalisar dattijan ta dakatar da zaman su har zuwa ranar 16 ga Janairu, 2019

Majalisar Dattijai ta Najeriya ta dakatar da zaman su har zuwa ranar 16 ga watan Janairu, 2019 bayan da Shugaban Majalisar, Ahmed Lawan ya bada shawarar a yi hakan, a yayin da suka gama ganawar su ta ranar Alhamis.

Yayin da shugaban, Mista Lawan  ke bada wannan shawarar,  ya gode wa abokan aiki na adawa, ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya, ‘yan jaridu da sauran wadanda suka goyi bayan Majalisar ta samun nasara a 2018 ‘.

7. Saraki yayi karar Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya don aiwatar da yajin aiki

Shugaban Sanatocin, Bukola Saraki yayi karar ma’aikatan majalisar dokoki don shiga yajin aiki akan rashin karban albashi.

A wata bayani daga shugaban kungiyar NASS ta Nijeriya a birnin Abuja, an bada umurnin a dakatar da yan Kungiyar Ma’aikatan Majalisar daga yajin aiki da suka fara a karkashin jagorancin kungiyar (PASAN).

8. Shugaba Buhari zai karbi rahotannin AFCFTA a watan Janairun 2019

Kwamitin Gudanarwar Shugaban kasa a Yankin Harkokin Ciniki na Afirka (AfCFTA) zata bada rahoton shawarar su ga shugaba Muhammadu Buhari a watan Janairu 2019.

An sami wannan gabatarwa ne daga bakin Mallam Garba Shehu, babban magatakarda na musamman ga shugaban kasa, a wata bayyanin da aka sanya hannu a ranar Alhamis 20, ga Watan Disamba, 2018.

9. APC ta dakatar da shugabannan Jam’iyyar a Jihar Imo da Ogun

Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar APC ta dakatar da shugabannin jam’iyyar su na jihar Imo da Ogun.

Gidan yada Labarai na Naija News ta sami wannan tabbaci ne cewa Sakataren Yada Labarun na jam’iyyar, Isah Lanre-Onilu, ne ya bada wannan rahoto  a ranar Jiya.

10. Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya umarci janye sojojin Amurka daga Syria

Shugaba Donald Trump ya bada umarnin janye sojojin Amurka daga Syria.

An sami tabbaci daga wani ma’aikaci na US bayan Shugaba Trump ya yi iƙirarin cewa Amirka ta ci nasara da yan ISIS ga yakin basasa a kasashen.

Samu cikakun labarai daga Naij News Hausa