Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Yan ta’addan Boko Haram sun kai Farmaki a Chibok

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A daren jiya, ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai farmaki a Makalama, wata kauyen garin Gatamwarwa, dake karamar Hukumar Chibok, a Jihar Borno.

“Sun fado wa kauyen ne da daren nan, (watau jiya Lahadi) ta wata kauye da ke kusa damu, watau Gogumdi,” in ji bayanin wani mazaunin karkaran Chibok, a yayin da yake gabatarwa ga manema labarai.

“Sun shiga harbe-harbe mutane ko ta ina ba mafari. a halin yanzu mutane zun gudu sun kuma fada wa gadun daji don neman buya. Sojojinmu a nan na jagorancin 117 bataliya na a shirye don fada masu,” in ji Shi.

yankin Makalama na da kimanin kilomita 21 daga garin Chibok.

“Da dama daga cikin ‘yan kyauyen manoa ne duka, kuma suna cikin lokaci ne na girbi. ‘Yan ta’addan su fado wa mutane da harbe-harbe ne, da kuma mutane suka ga haka, sun fada wa daji da gudun don neman sauki. ‘Yan ta’addan kuwa suka bi kayan su da banna da dauke-dauke”. Inji wani mazaunin garin Chibok a bayanin sa da manema labarai.

Sani Usman, kakakin sojojin, ya ce sojojin sun mayar da martani ga harin a halin da ake ciki yanzun nan.

Ko da shike sojoji na karafa da kokarin ganin cewa sun yi yaki da gaske da wannan farmakin, har wa yau al’umma Borno duka sun saura cikin kangin yan Boko Haram. inji fadin Abubakar Elkanemi, Shehun Borno a Watan Nuwamba da ta gabata.

 

Naija News ta ruwaito ‘Yan Ta’adda sun kai wata sabuwar a kauyuka biyu ta yankin Magaji, a Jihar Zamfara.