Connect with us

Uncategorized

Gwamna Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya ziyarci wasu sojoji da aka yiwa raunuka

Published

on

at

advertisement

Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara ya kai ziyara ga sojojin da aka yiwa rauni a wani harin da wasu Mahara  suka yi kai masu a ranar Asabar da ta gabata.

Rahoto ta bayas cewa Sojojin sun fara samun sauki a yayin da ake masu kulawa a yanzu, a asibitin Tarayya ta Gusau, babban birnin Zamfara.

Sanusi Rikiji, mai magana da yawun majalisar dokokin jihar da kuma shugabannin jami’an tsaro na jihar ya tafi ne tare da Gwamnan a wannan ziyarar .

“Gwamnan Jihar Zamfara da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Hon. (Dr) Abubakar a ranar Lahadi 30 ga watan Disamba, 2018 sun yi ziyarar nuna bacin rai da tausayawa ga jami’in sojoji bakwai da aka jikkata a wannan yaki da Mahara da suka yi a Dajin Dumburum a yankin Zurmi”. daga sanarwar.

“Gwamna ya ziyarce su ne don duban lafiyar su da kuma neman sanin yadda suka karu da samun kulawa a Asibitin Tarayya na Gusau”.

Bayyan ganin wannan,  yace “Ya tabbatar masu da cewa gwamnatinsa za ta ba da gudummawa ga tabbatar da zaman lafiyar jami’an tsaro, kuma nuna masu goyon baya don karfafa su a yakin basasa da sauran ayyukan ta’addanci a jihar.”

A cewar Majiya, tashin hankali a Jihar ya kawo rasuwar rayuka kimanin mutane 3000 cikin shekaru biyu a halin yanzu.

Mataimakin Gwamna Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala, ya yi zargin cewa Shugabansa, Abdul’Aziz Yari ya ba da hadin kai ga wannan.

Naija News ta ruwaito da cewa Mahara sun kai wata sabuwar hari a kauyuka biyu ta yankin Magaji, a Jihar Zamfara a ranar 21 ga Watan Disamba, 2018.

Karanta Kuma Yan Kungiyar HISBA a Jihar Kano sun kama wasu ‘Yan Mata Goma sha daya 11 da zargin shirin yin aure na jinsi daya, watau Mace-da-Mace.