Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Litinin 31, ga Watan Shabiyu, a Shakara ta 2018

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin 31, ga Watan Shabiyu, 2018

1. Gwamnatin Tarraya za ta cigaba da tunawa da Shehu Shagari

Gwamnatin tarayya ta yi alkawalin cewa za ta maye gurbin tsohon shugaban kasa, Alh. Shehu Shagari wanda ya mutu a ranar Jumma’a a birnin Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi wannan alkawarin ne a ranar Lahadi a Sokoto lokacin da ya je ta’aziyya ga dangin tsohon shugaban ta Najeriya.

2. ‘Yan sanda sun gabatar da kama Sanata Dino Melaye

Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun gabatar da shirin su na shiga gidan zama na dan majalisar, Sanata Dino Melaye a Abuja don kama shi.

Kakakin ‘yan sandan, Jimoh Moshood, ya ce an shiga gidan dan majalisar dattawan don neman kama shi ga wata laifi da ya auka.

3. Dangote ba ya cikin masu jagoranci lamarin Takarar Shugaban kasa ta Jam’iyyar APC – in ji shugabancin

Ofishin shugaban kasa tayi murabus da fadin ta na cewa Mai arzikin na Afrika, Aliko Dangote na daya daga cikin yan Jam’iyyar APC dake gudanas da kampen na Jam’iyyar ga zaben 2019.

A cewar shugabancin, Dangote ba zai iya kasancewa memba na kwamitin yaƙin neman shugabancin ba saboda ba shi da katin zaman mamba na jam’iyyar.

4. Ambode ya zabi Muri-Okunola a matsayin sabon HOS Legas

Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode a ranar Lahadi, ya amince da nada Mr Hakeem Muri-Okunola a matsayin shugaban HOS na 21 ta Jihar.

Babban Sakataren Gwamnan, Mista Habib Aruna, ya bayyana cewa a nada Muri Okunola ne bayan da Mrs. Folasade Adesoye tayi ritaya a ranar 27 ga watan Disamba.

5. Katunan zaman dan Kasa kimanin 300,000 na a shirye don karba

Hukumar Gudanar da Katin Zaman Dan Kasa (NIMC) ta bayyana cewa fiye da 300,000 na ashirye don karba ga wadanda suka yi rajista tun shekarar 2012.

Mai magana da yawun Hukumar NIMC, Loveday Ogbonna, ya bukaci wadanda suka yi rajista cikin shekarar 2012 har zuwa watan Agusta na 2013 su je su karbi katunan su da wuri.

6. Jam’iyyar PDP ta ce bata amince da yin amfani da fasahar python ba ga zaben 2019

Kungiyar Shugabancin Jam’iyyar PDP (PPCO) ta ce bata amince da shiri na sabon Jami’an tsaro ‘Python Dance’ ba ga shirin zaben 2019 wanda Shugaban Jami’an tsaron sojoji na Najeriya, Tukur Buratai ya gabatar.

Sun bayyana cewa wannan shiri ne na ‘yan Jam’iyyar APC don yin amfani da dakarun sojoji wurin taune ko kuma yin halin magu-magu ga zaben 2019.

7. Tambuwal ya bada hutu ga al’umma Jihar sa sanadiyar mutuwar Shagari

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya gabatar da hutu ga al’umma Jihar a ranar Litinin 31 ga Disamba, musamman ga yin du’a’i da mutuwar tsohon shugaban kasar, Shehu Shagari.

An samu wannan bayanin ne daga Daraktan Sanarwa na gwamnan, Malam Abubakar Shekara, a wata sanarwa da ya gabatar ga manema labarai a ranar Asabar a Jihar Sokoto.

8. Uzor Kalu ya bayyana dalilin da ya sa yayi murabus da PDP ya koma Jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan Jihar Abia, Chief Orji Uzor Kalu ya bada cikakkun bayanai da tattaunawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari kafin ya koma jam’iyyar APC.

Kalu wanda ya jagoranci Jihar Abia, daga watan Mayu 29, 1999 zuwa Mayu 29, 2007 ya ce ya bar Jam’iyyar APC ne bayan da Buhari ya yi masa alkawarin zai kammala wasu ayyuka na musanman a Gabas ta Jihar.

9. Dan Majalisar wakilai na Jihar Legas, Abayomi Ayeola ya mutu

Wani dan majalisar wakilai dake wakiltar yankin Ibeju Lekki na Jihar Legas, Mr Abayomi Ayeola, ya mutu.

Ayeola ya rasu ne da yamma, a ranar Lahadi a wata asibiti mai suna St. Nicholas a Legas bayan rashin lafiya na yan lokatai.

10. Na ki amince da kudi kimanin Dala Miliyan 5 ($5m) na cin hanci daga Jonathan – in ji Hamzat

Mataimakin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar Legas, Obafemi Hamzat, ya yi zargin cewa ya ki amincewa da cin hanci da rashawa na dala miliyan 5 daga hannun tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a lokacin zaben 2015.

Ya bayyana cewa ya ki amincewa da kudin ne saboda yana tunanin gaba, da kuma neman kada a bata masa suna.

Samu cikakkun labarai a Naija News Hausa