Connect with us

Uncategorized

Ba Gwamna Nasir Elrufai muke wa aiki ba – Shehu Usman Dan Tudu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kungiyar hadin gwiwar tsaro (CJTF) na Jihar Kaduna, Shehu Usman Dan Tudu ya bayyana a ranar Talata da cewa kungiyar ta su ba gwamnan jihar, Nasir El-Rufai suke yi wa aiki ba, domin kungiyar tasu ba ta siyasa ba ce.

Yace cewa abu mafi fifiko ga kungiyar tsaron ta su ita ce ganin kare jama’arsu ba domin wata  jam’iyyar siyasa ba.

Shugaban Kungiyar, Shehu Dan Tudu ya bayyana wannan ne da yake bada bayani ga manema labarai a wata ganawa na Hidimar murnan Sabuwar Shekara da cibiyar kula da zaman lafiya da sulhu ta Najeriya ta shirya a Hadaddiyar kungiyar Manema Labarai ta Najeriya (NUJ) a nan Jihar.

Ya bayyana cewa fade-fade da labaru akan kungiyar a cikin Jihar ba gaskiya bace, duka labarin karya ne.

Shugaban ya bayyana cewa, a matsayin rukuni, gurin su ita ce samar da tsaro da kuma ganin kare lafiyar mutanen Jihar daga ta’addanci na kowace iri.

“Ba mu gudanar da aiki ga Jam’iyyar PDP; kuma ba mu gudanar da aiki ga APC ko wata jam’iyyar siyasa a Jihar. Mu kawai Kungiyar JTF ce ta farar hula da gurin kare al’ummar Jihar daga ‘yan ta’adda duka”.  in ji Shugaba.

“Dan mun halarci taron Jam’iyyar APC bai bayyana cewa muna aiki ne a gare su ba, domin kuwa idan Jam’iyyar PDP ko wata jam’iyya ta gayyace mu don samar da tsaro gare su, za mu tafi wannan taron mu kuma gudanar da aikin mu”.

“Za mu kasance tsaka tsaki a kullayomi. don haka, ba mu aiki ga gwamnan Jihar, duk wata rahoto da ke zagaya a Jihar ba gaskiya ba ne”, inji shi.

Naija News ta ruwaito da cewa Yara kimanin 132 suka mutu a Jihar Kaduna don rashin samun isashen abinci