Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Laraba 2, ga Watan Janairu, a Shakara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba 2, ga Watan Janairuyu, 2018

1. Kungiyar Labour Congress (NLC) sun yi barazanar shiga yajin aiki

Kwamishinan Jakadancin Najeriya (NLC) a jiya ya sake bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da gudanar yajin aiki ganin kasawar gwamnati ta rashin aiwatar da sabon albashi na N30,000 ga ma’aikatan Najeriya.

Wannan Ƙudurin ya kansance ne ganin cewa gwamnati taki aiwatar da arjejeniya bisa gudanar da sabon tsarin albashi.

2. ‘Yan Shi’a sun halarci hidimar murnar sabuwar shekara a cocin Katolika

‘Yan Kungiyar musulunci na Najeriya da aka fi sani da suna, ‘Yan Shi’a sun halarci hidimar sabuwar shekarar 2019 a wata Iklisiya a Zariya, Jihar Kaduna, don karfafa haɗin kai tsakanin ‘yan kasa duka.

Kungiyar ta halarci hidimar ne a St. Mary’s Parish Church, Samaru, Zaria, Jihar Kaduna a ranar jiya.

3. Atiku ya yi matukar damuwa a kan yanayin rashin aiki ga matasan Najeriya

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yayi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bisa yanayin rashin aiki da kuma ganin kimanin ‘yan Najeriya fiye da miliyan 90 dake cikin talauci a karkashin mulkin.

Atiku ya kuma karyace Shugaba Buhari don fadin sa ‘yan kwanaki kadan da ta gabata a garin Uyo, babban birnin Akwa Ibomna cewa ya cika dukan alkawuran da ya yi kamin aka zabe shi.

4. NLC ba ta yi zurfin tunani ba game da farashin kudi na N30,000 – Gwamnoni

Gwamnonin jihohi 36 na tarayya a ranar Litinin sun bayyana matakin Kwamitin Kasuwanci ta Nijeriya (NLC) da cewa wannan neman karin kudi ta Naira dubu 30 hanya ce na raunana kasar.

Gwamnonin tarayyar sun bayyana da cewa ba za su iya biyan wannan kuɗin ba kamar yadda Hukumar NLC ta buƙace su da ida.

5. Zaben shekara 2019 ba al’amarin Yi ko Mutuwa – Buhari

Shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tabbatar da gudanar da zabe mafi kyau a shekara ta 2019, kuma bada gargadi ga ‘yan siyasa duka kada su mai da zaben kamar abin dole ko ga mutuwa.

Wannan shi ne daya daga sakon sabon shekara da shugaban kasar ya bayar ga jama’ar Najeriya a ranar farko ta sabon shekara.

6. Ezekwesili tayi alkawarin inganta tattalin arzikin Najeriya idan a zabe shi zaman shugaban kasa

Dokta Obiageli Ezekwesili, dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar Allied Congress of Nigeria (ACPN) ta bayyana tsarin ta na inganta kasar idan har an zabe ta. Ta bayyana wannan ne a sakon sabuwar shekara da ta yi ga ‘yan Nijeriya.

Ezekwesili, Ta yi alkawarin inganta tattalin arzikin Najeriya a hanya mafi mahimmanci a fadin Afrika duka, ta ce idan an gudanar tattalin arzikin Najeriya a hanyar da ta dace, kasar zata zama da wadata bisa sauran kasashe na Afirka duka.

7. Shugaba Buhari ya sadaukar da kansa ga kawo Kungiyar Boko Haram ga karshe – Gwaman Borno

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa ganin irin sadaukarwa da Shugaba Muhammadu Buhari yayi akan kawo karshen tashin hankalin da ake a Arewa maso Gabas na Jihar, shine dalilin da ya sa bai zargi shugaban ba har wa yau.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da ya gudanar da wata taron “tsaro mafi daban” a babban birnin jihar watau Maiduguri a ranar Talata, don magance hare-haren da ake yi ga Jami’an tsaro a Jihar.

8. Sanata Dino Melaye ya yi alkawarin kasance a ɓoye ga ‘Yan sanda

Sanata Dino Melaye ya ce ba zai mika kansa ga ‘yan sanda Najeriya ba da yadda suka nuna bukatar kamashi ga wata laifi da ake zargin sa da aukawa.

Ya gabatar da wannan ne wasikarsa a shafin twitter inda ya ce akwai bambanci tsakanin taurarewa da kuma hikima.

9. Ofishin kadamarwa ta Amirka ta ce za ta ci gaba da yin bincike na takadar VISA

Ofishin kadamarwa ta Amirka a Nijeriya ta sanar da cewa ofisoshinsa dake a birnin Abuja da birnin Legas na a bude ga dukkan kasuwanci.

An tabbatar da wannan ne a wata sanarwa da suka aika ta shafin yanar gizon ta da kuma shafin nishadarwar ta a ranar Sabuwar Shekara, suna kira ga jama’a dake ke neman aiki su halarci ganawar su.

10. An anbaci Orji Uzor Kalu a zaman daya daga yan kungiyar gudanar da neman zabe na Buhari

Duk da cewa Hukumar Tattalin Arziƙi na Kasa (EFCC) na zargen shi da cin hanci da rashawa na Naira biliyan N7.7,  An nada tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu a cikin kwamiti na neman zaben karo ta biyu ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Samu cikakun labarai a Naija News Hausa