Labaran Nishadi
‘Yan Sanda na balle mani kofa – Sanata Dino Melaye
Sanata Dino Melaye, Sanata da ke wakiltar Jihar Kogi yayi kira ga jama’a cewa ‘Yan Sandan Najeriya sun hallaro a gidansa da safen nan da motocin su da kuma kayaki da zasu balle masa kofa da ita.
Sanatan ya sanar da wannan ne a sashen nishadi ta twitter.
Sakon na kamar haka, a turance;
Police bringing in tool boxes to break doors and vandalize my house. Police EOD truck just brought them. Media take note
— Senator Dino Melaye (@dino_melaye) January 2, 2019
Lokatai kadan a baya, Melaye ya yi alkawarin ba zai mika kansa ga ‘yan sanda ba, yayi kwatantawar kansa da Annabi Iliya na Littafi Mai Tsarki cewa akwai bambanci tsakanin tsorata da nuna hikima.
Kwatancin sa na a haka, a turance;
The Bible record prophet Elijah to be among one of the strongest prophets that lived,but he went to mount Carmel to hide when king Ahab sought him to kill him cos of the way he boldly declared the truth. There is a difference with being scared and being wise.
— Senator Dino Melaye (@dino_melaye) January 1, 2019
Da farko dai ‘yan sanda sun yi rashin amincewa da zargin mamaye gidansa, amma daga bisani sun amince da cewa Jami’an tsaron na bincike da kuma neman kama Sanata Dino Melaye akan wata laifi da ya auka.
Sanatan, shi ma a kwanan baya ya tayar da ƙararrawa cewa IGP, Ibrahim Idris ya ba da umarnin a kama shi bayan haka ya yi niyyar yi masa alurar mutuwa da wata muguwar kwaya.
‘Yan sanda suna lura da gidansa tun lokacin da aka kai harin a ranar Laraba, amma har yanzu ba a kama shi ba.
‘Yan Sanda sun rigaya sun mamaye gidan Sanatan tun ranar Laraba da ta gabata, amma har ila yau basu samu daman kama sanatan ba.
Naija News ta ruwaito Sanatoci sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari tsuwa a yayin da yake bada Kasafin kudi na 2019