Uncategorized
Ba mu da shirin yin Makirci ga zaben 2019 – INEC na gayawa PDP

Ba mu da shiri ko niyar yin makirci a zaben 2019 da ke gaba – inji Hukumar INEC
Hukumar shirin zabe (INEC) ta karyace zargin da ‘yan Jam’iyyar PDP ta yi da cewar Hukumar na da shirin makirci ga zaben 2019 da ke gaba.
Babban Darakta na Yadar da labarai na Kwamitin Gudanar da shirin zaben na Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ba da shawara a wani taron manema labarai a ranar Laraba cikin birnin Abuja.
Ologbondiyan ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na a sane da cewa shugaban kwamitin na gudanar da zabe , Farfesa Mahmood Yakubu na cikin masuwa da gabatar da sakamakon zabe a dukan mazaba kamar yadda yake a dokar samar da sakamakon zabe.
Ya kara da cewa nuna sakamakon zabe a rumfunan zabe ya kasance ainihin sakamako ta gaske, kuma kuma wannan ya zama daya da wanda hukumar zata sanar a yayin da take gabatarr da sakamakon ta na’urar lantarki na hukumar INEC, da tabbacin cewa ba a taune zabe ba ko nuna makirci.
“Kada Farfesa Yakubu ya tsoma kansa ga hitinar shugabancin Buhari, domin yin haka zai sa shi cikin wata mumunar hali ga ‘yan Najeriya”. in ji shi.
Duk da haka dai, Babban Sakataren hukumar INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ya karyata wannan zargin Jam’iyyar PDP ga cewa hukumar na da muradin yin makirci ga zaben 2019, kuma ya bukaci Jam’iyyar PDP ta ba da hujjoji ga wannan zargin idan har hakan ne.
Naija News ta ruwaito da cewa hukumar gudanar da Zabe, INEC ta ce “za mu gudanar da zaben 2019 tare da dokokin da ake da ita