Connect with us

Uncategorized

Jihar Katsina na cikin kangin ‘Yan Hari – Gwamna Masari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A jiya Laraba 2 ga watan Janairu 2019, Gwamnatin Jihar Katsina ya daga murya da cewa, ‘yan fashi, barayi da masu satan mutane sun mamaye Jihar.

Wannan shine bayyanin Gwamnan, Aminu Masari a yayin da yake gabatarwa a wana bikin ganawa da ya yayi a Jihar Katsina da Jami’an tsaron Jihar duka.

“Al’umman Jihar na fuskantan mumunar hari a koyaushe daga wadannan ‘yan harin da ‘yan ta’addan da ke a Jihar”

“Jiharmu a halin yanzu tana cikin mawuyacin hali da irin hari da sace-sacen mutane da ake yi, Idan har suka kame mutum, sai su bukaci kudi kuma idan har ba a samu biyar kudin ba, sai su kashe wannan da ke a kame”. in ji Gwamnan.

Naija News ta ruwaito cewa wasu yan hari sun harbe Tsohon ofisan tsaro, Alex Badeh har ga mutuwa

Gwamnatin Katsina ta shirya hadadiyar taro na hadin gwiwar jami’an tsaro duka don don magance wadannan matsalolin da ake fuskanta a Jihar.

Jama’ar Jihar Katsina da ke kananan hukumomin 34 a halin yanzu suna barci ne da ido daya bude da kuma ido daya a rufe. Matafiya na tsoron a tare su kan hanya da kuma kama tsoron kada ‘yan fashi ko masu satan mutane su kame su da bukatan sai har an biya kamin a sake su. Jihar na cikin mawuyacin hali a halin da ake ciki yanzun nan” inji Masari.

Ya kara da cewa abin da mummunar ji har ma da cewa ɓarayi sun sace wasu kayan lantarki kusa da Gidan Gwamnatin da ke a GRA a Jihar Katsina.

“Ina kira ga dukan masu ruwa da tsaki su fito da hanyoyin da zai taimaka wa jami’an tsaro don aiwatar da ayukan su yadda ya da ce”. inji shi

Gwamnan ya shawarci masu ruwa da tsaki cewa kada su boye duk wani mai laifi ko dan ta’adda, su kuma bayyana duk wani muhimman abu a wannan ganuwar.

Gwamnan ya kara da cewa a halin yanzu ya kamata mu iya sadaukarwa da zai sa mutanen Jihar mu su sami kwanciyar hankali da zaman lafiya har ma su iya aiwatar da sana’an su yadda suka saba yi a kullum ba tare da wata tashin hankali ko tsoro ba.

Karanta kuma: Ba Gwamna Nasir Elrufai muke wa aiki ba in ji Shehu Usman Dan Tudu Shugaban CJTF