Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Alhamis 3, ga Watan Janairu, a Shakara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 3, ga Watan Janairu, 2018

1. Rochas Okorocha ya ce ba gaskiya bane cewa na bar Jam’iyyar APC zuwa  AA

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa karya ne da cewar ya na da’awar shirin sanar da barin jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar AA.

A cewar wata sanarwa, gwamnan ya yi zargin cewa ya janye daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar surukin sa Uche Nwosu.

2. Mbaka ya gabatar da nuna goyon bayan sa ga sake zaben Buhari

Babban shugaban Iklisiya ta ‘Adoration Ministry’, Ejike Mbaka ya bayyana goyon bayan sa ga shugaba Muhammadu Buhari ga zabe ta gaba.

Babban malamin ya gabatar da wannan goyon bayan na sa ga Shugaba Buhari ne a sakon sa ta sabuwar shekara.

3. Jihar Katsina na a cikin kangi – in ji Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari yayi kukar kirar taimako a ranar Laraba da cewa a halin yanzun na, jihar na cikin kangin ‘yan hari, da ‘yan fashi da kuma masu sace mutane.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin bikin bude taron koli na tsaro a Jihar Katsina da sojoji, ‘yan sanda, da jami’an tsaron DSS da kuma sauran jami’an tsaro  da ke Jihar har da Mallaman gargajiya ta Jihar.

4. Gwamnatin tarayya ta ba da biliyan N15.8bn zuwa jami’o’i don karshe yajin aikin ASUU

Yajin aikin kungiyar ASUU da aka farasa watannai da dama da suka shige zai ƙare a yayin da gwamnatin tarayya ke nuna kulawa don ganin cewa ASUU ta karshe yajin aikin.

Za a gudanar da wannan da’awar a gaban shugan kungiyar a ranar litini ta gaba wanda shugan kungiyar ma’aikata, Chris Ngige zai wakiltar.

5. IGP ya tsige kwamishinan ‘yan sandan na Jihar Imo tare da wasu

Shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris ya shashake ‘yan saron Jihar Imo a yayin da ya tsige kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Dasuki Galadanchi da wasu manyan jami’an tsaron Jihar.

Shugaban ya kuma tsige mataimakan Kwamishinan ‘yan sanda ukku da ke shugabancin tsaron yankin yaki da ta’addanci a Jihar.

6. Dalilin da ya sa Buhari ya kafa kwamiti kan sabon albashi

Ministan kasafi da Shirye-shiryen kasa, Sanata Udo Udoma ya ce shugaban kasar, Muhammadu Buhari na a shirye don aiwatar da karin farashin kudi mafi daidanci.

Ministan, ya gabatar da wannan ne a yayin da yake jawabi wurin bada kasafin shekara  ta 2019. Ya bayyana cewa an riga an kafa kwamiti na fasaha mai karfi don samar da hanyoyin da kuɗi za su fito don tallafawa wajen biyan sabon farashi da kuma taimakawa wajen rage lalacewar tasirin arziki a yayin da za a fara gudanas da sabon farashin.

7. Rundunar Sojojin Najeriya sun bukaci kame likitan da ke gudanar da neman kudade don taimakawa dakarun sojojin

Rundunar sojin Najeriya ta janye kanta daga shirin samar da kudade don taimakawa ga ciyar da dakarun da ke yaki da ‘yan Boko Haram a kasar.

Babban daraktan sanarwa da yadarwa rundunar sojojin, Brigadier General Sani Usman ya gabatar da wannan a wata sanarwa da aka yi a ranar 2 ga watan Janairu 2019.

8. Sanata Dino Melaye na zargin ‘yan sanda da kokarin balle kofofin gidan

Sanatan na Jihar Kogi, Dino Melaye ya tayar da murya da safiya, da zargin cewa ‘yan sanda sun zo cike a mota da akwatunan kayan aiki don balle masa kofofin gidansa.

Sanatan ya bayyana wannan ne a yanar gizon twitter.

9. ASUU ta musunci fadin cewa Gwamnatin Tarayya ta ba kungiyar kudi N15.8b don karshe yajin aiki

Cibiyar Jami’ar ta ce ba ta da wata sani a cewar an biya Naira biliyan 15.89bn ga Jami’o’i da don karshe yajin aikin da aka fara watanni biyu da ta gabata.

Shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labaru a ranar Laraba a birnin Legas.

10. Nnamdi Kanu ya yi kira ga magoya bayan kungiyar IPOB su kauracewa zaben 2019

Shugaban, da ke Jagoran al’ummar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu, ya yi kira ga dukkan iyamirai da cewa su kauracewa zaben shekarar 2019. ya bayyana wannan ne a cikin sakon sa na sabuwar shekara da ya bayar a gidan labarai a ranar jiya.

Samu karin labarai ta Najeriya akan hausa.naijanews.com