Connect with us

Uncategorized

Tsohon Minista, da Kuma tsohon Gwamnan Kano Hamza Abdullahi (rtd) ya Mutu

 

Ga sabuwa: Tsohon Minista na Babban Birnin Tarayya (FCT) a lokacin shugabancin Janar Ibrahim Babangida (Rtd.) mai suna Air Hamza Abdullahi (Rtd.) Ya mutu.

Tsohon, dan shekaru 73 ya yi shugabanci a matsayin gwamnan na Jihar Kano a karkashin shugabancin shugaba Janar Muhammadu Buhari (Rtd) daga shekara ta 1984 zuwa shekarar 1985.

An samu tabbacin mutuwar ne daga bakin Ofisan yad labarai na hukumar Hadejia, Mohammed Garba Talaki. Mohammed ya ce, “Tsohon ya mutu ne a asibitin Jameni bayan da yayi rashin lafiya na ‘yan lokatai a ranar Alhamis” in ji shi.

Marigayi Abdullahi, dan haifuwan garin Hadejia ne na Jihar Jigawa, kuma an haife shi ne a ranar biyu 2, ga watan Maris na shekarar 1945. Marigayin ya mutu da barin Mata uku da yara da dama.

Abdullahi yayi karatu ne a makarantar Sojojin Sama ta Najeriya da ke a birnin Kaduna a shekara ta 1964, daga nan ya sami daukakawa har zuwa matsayin (Air Vice Mashal) a watan Aktoba, shekara ta 1988, kuma ya huta daga shugabancin bayan wata biyu da aka kara masa girma a Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya.

 

Naija News ta ruwaito da cewa wasu yan hari sun harbe Tsohon ofisan tsaro, Alex Badeh har ga mutuwa

Advertisement
close button