Connect with us

Labaran Najeriya

Ba za ku koya mana aikinmu ba – INEC ta gayawa Jam’iyyar PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar INEC ta mayar da martani ga jam’iyyar PDP a kan zaɓan Amina Zakari

Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) a ranar Alhamis ta gargadi ‘yan jam’iyyar PDP da cewa su yi shiru da ƙoƙarin nuna iyawa da koya wa hukumar aikin ta.

A cewar hukumar, Jam’iyyar PDP ba zata umurce mu ba da hanyar da zamu gudanar da zaben 2019 ko kuma wanda zamu sanya a kowani matsayi ba.

Rotimi Oyekanmi, Babban Sakatare yada labarai (CPS) ga Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya umurci ‘yan Jam’iyyar PDP da cewa ta dakatar da duk wata fade-faden ta ga hukumar akan sanya Amina Zakari Kwamishanan Tarayyar.

Hukumar ta mayar da martani ne ga rashin amincewar Jam’iyyar PDP ga zaben Amina, da cewa Amina Zakari dangi ce ga shugaba Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar kuma ta ce wannan nadin hanya ce na aiwatar da makirci don ganin shugaba Buhari ya ci nasara ga zaben 2019.

Naija News ta ruwaito da cewa Hukumar zabe, INEC ta nada kwamishinan kasa Amina Zakari a matsayin shugaban cibiyar gudanar da karban zabe ta shekarar 2019.

Oyekanmi ya ce, Shin menene matsalar wannan matar? menene kuke da ita? laifin me ta ke da shi?

Amina ta fara shugabanci ne tun lokacin shugabanci tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, duk wata matsala da ta ke da shi ta yi shine tun Jam’iyyar PDP na mulki shekaru da suka gabata.

“Matar ta na da iyalin ta, da yaran ta amma Jam’iyyar PDP ta cigaba da muzurna ta. na tabbatar cewa babu wanda zai ji dadi a cikin su idar har an yi wa matar su wannan kiyayya”. in ji Oyekanmi a bayyanin sa da manema labaran Independent.

Ba Amina ba, ko Shugaban gudanar da zabe tarraya gaba daya bai isa ya yi makirci ga wannan zaben ba. to menene damuwar ku? in ji Rotimi.

Karanta kuma: Jirgin Sojojin Sama da ke taimakawa ga yakin Boko Haram ta fadi