Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Jumma’a 4, ga Watan Janairu, a Shakara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a 4, ga Watan Janairu, 2019
1. PDP ta nacewa yin amfani da na’urar katin zabe ga zaben 2019
Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP ya lura sosai kuma da nuna damuwa ga cewa hukumar zabe na shirin daukar matakin yin amfani da takarda kawai wajen gudanar da zaben 2019.
Mai ba da shawarar labaru ga Atiku Abubakar, Paul Ibe ya ce duk wata shawarar ko da’awar yin amfani da takardar zabe kawai ba tare da yin amfani da na’urar duba katin zabe ba, Jam’iyyar su ba za ta yadda da irin wanan matakin ba ga zaben watan Fabrairu 16, 2019.
2. Hukumar INEC ta nada Amina Zakari a matsayin shugaban cibiyar karban zabe
Hukumar zabe, INEC ta nada kwamishinan kasa Amina Zakari a matsayin shugaban cibiyar gudanar da karban zabe ta shekarar 2019.
Amina za ta jagoranci kwamitin cibiyar kula da kuma karban zabanni. Wannan daya ne daga cikin kwamitoci biyu da Shugaban gudanar da zaben, Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar a ranar Alhamis a birnin Abuja.
3. Jihohi ba su nuna goyon baya ba ga Buhari don yaki da cin hanci da rashawa
Lauyan damar Al’umma, Femi Falana SAN ya gabatar da cewa Najeriya ba ta a shirye don yaki da cin hanci.
Falana, ya bayyana da cewa Jihar Kano ne kawai a cikin dukkan Jihohin tarayya ta kafa kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, ya kara da cewa babu wata Jiha da ta nuna kiyaya ko mahinmancin ga yakin cin hanci da rashawa.
4. Zanyi murabus da matsayi na a gwamnan jihar Zamfara a kan kashe-kashen da ke aukuwa – Gwmana Yari
Abdulaziz Yari, Gwamnan Jihar Zamfara ya ce yana shirye ya sauka daga matsayinsa na Gwamnan Jihar, idan har kafa dokar dakatar da ayuka a Jihar don halin bacir tsaro da ake ciki.
Gwamnan wanda ya nuna bukatar a sanar da dokar ta baci don magance kisan kai da ke aukuwa a Jihar arewa maso yammaci ya ce, wasu ‘yan siyasa ne su ka bada shawarar hakan da duban cewa gwamnan na jin tsoro ya rasa ofishinsa.
5. Kotu ta ki amincewa da bukatar ‘yan sanda su bar gidan Sanata Dino Melaye
Babbar Kotun Tarayya da ke a birnin Abuja ta ki amincewa da wata takardar neman umarni don ‘yan sanda su jaye jami’an tsaron su daga gidan Sanata Dino Melaye dake a birnin Abuja.
Mai Shari’ar, Jastis N.E Maha ya ki amincewa da wannan takardar neman izinin jaye jami’an tsaro da Melaye ya rubuto, da cewa sai har a kai ga maƙasudin karar.
6. Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da nadin Amina Zakari a matsayin shugaban karban zabannai a shekarar 2019
Wannan sabon nadi da aka yi wa Amina Zakari a matsayin shugaban karban zabunan zaben 2019 ya zama abin rashin amincewa da ga Jam’iyyar PDP.
Jam’iyyar da ta bayyana da cewa Amina dangin shugaba Muhammadu Buhari ce, dadin ta ga wannan matsayi zai kawo tashin hankali.
7. Kotu ta ba da beli ga ‘yan fadan Biafra 51
Kotun Koli ta Jihar Abia ta ba da beli ga ‘yan kungiyar guda 51 da aka kama kwanakin baya, an bada belin ne kwanaki kadan kafin Kirsimeti a garin Umahia ta Jihar.
‘Yan kungiyar da aka kama su kwanakin baya ta kumshi mata goma da wasu tsofaffi da dama da ake zargi da halin ta’addanci na kungiyar IPOB da kuma zargin kadamar da ayukan da ba ta dace ba.
8. Jami’an Sojojin sama NAF ta rasa Ofisoshi 5 ga hadarin jirgin sama a wajen yakin Boko Haram
Rundunar jami’an tsaron ta Sojojin Sama na Najeriya ta samu ribato gawar Ofisoshi biyar da suka rasa rayukan su a hadarin jirgin saman sojojin Najeriya (NAF) Mi-35M Helicopter wanda ya fadi a fagen yaki da ‘yan Boko Haram a ranar 2 ga watan Janairun 2019 a Damasak ta Jihar Borno .
Ibikunle Daramola, Daraktan yada labarai na jami’an tsaron ne ya bada wannan rahoton a wata gabatarwa.
9. Ba za ku koya mana aikinmu ba – INEC ta gayawa Jam’iyyar PDP
Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) a ranar Alhamis ta gargadi ‘yan jam’iyyar PDP da cewa su yi shiru da ƙoƙarin nuna iyawa da koya wa hukumar aikin ta.
A cewar hukumar, Jam’iyyar PDP ba zata umurce mu ba da hanyar da zamu gudanar da zaben 2019 ko kuma wanda zamu sanya a kowani matsayi ba.
10. ‘Yan karatun Jami’o’in Najeriya sunyi barazanar kauracen wa zaben 2019 idan har yajin aikin kungiyar ASUU ta ci gaba
Shugaban kungiyar ‘yan Jami’an Najeriya NANS, Kamrad Danielson Akpan ya gargadi Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malamai Jami’a ASUU don su warware matsalar da ke tsakanin su kamin zaben da ke gaba a kasar.
Kungiyar ta ce idan har Gwamnatin taraya da ASUU bata bi wannan gargadin ba na kai ga yarjejeniya, lallai zasu kaurancewa zabe da ke gaba a kasar.
Samu cikakken labarai a Naija New Hausa