Connect with us

Labaran Najeriya

Zana’izar Tsohon Shugaba Shehu Shagari a Sokoto

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Allah ya gafarta masa

Anyi zana’zar Tsohon Shugaban Kasa, Shehu Usman Shagari wanda ya mutu a babban asibitin tarayya da ke a birnin Abuja. Tsohon ya mutu ne da shekaru 93.

Kadan daga Tarihin Tsohon Shugaban Kasar

Marigayi Shehu Shagari da aka haife shi a wata kauye mai suna Shagari wadda aka samar da wannan sunan kauyen ta wurin baban da ya haifi Shehu, mai suna Ahmadu Rufa’i sarkin kauyen Shagari. haka kuwa ya sanya wa iyalin suna Shagari.

Bincike ta bayar da cewa an haifi Shehu Shagari ne a shekara ta 1925 a kauyen Shagari.

“Tsohon Shugaban na daya daga cikin Manyan shugabanin kasar Najeriya. Shehu ya shiga lamarin Siyasa ne tun daga shekara ta 1951”.  an samar da wannan ne a wata yanar gizo ta Wiki.

Shagari bayan ya yi shugabanci da dama a kasar, ya sake fita takarar zaben shugaban kasa a shekara ta 1983 kuma ya ci zaben. Ko da shike bayan ya ci zabe, Janar Muhammadu Buhari ya daukin matakin tsige Shagari a ranar 31 ga watan Disamba a shekara ta 1983 kuma ya ci nasarar hakan.

Naija News ta ruwaito da cewa Farfesa Yemi Osibanjo ya ce so ta gaske Buhari ke da shi ga kasar Najeriya 

Karanta kuma: Ba mu da shirin yin Makirci ga zaben 2019 – Hukumar Zabe, INEC na gayawa Jam’iyyar PDP