Connect with us

Uncategorized

A kama wani dan Najeriya da sana’ar Miyagun kwayoyi a kasar India

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Uzoma, dan Najeriya da ke da shekaru 27 da haifuwa ya fada hannun ‘Yan Sandan kasar India

Jami’an tsaron India sun kame wani dan Najeriya da ke zaune a Gurgaon, Noida and Delhi-NCR nan kasar India, sun kame Joseph Uzoma ne da mugun kwayoyi na gram 37.5 da aka kimanta da kudi kimanin Rs 20 (kudin India).

Uzoma ya samu shiga kasar India ne da takardan shiga kasa (VISA) a matsayin dan makaranta, da ga nan sai ya fada wa sana’r sayar da mugayen kwayoyi. Ya bayyana da cewa ya kan biya wani mai mota don taimaka masa da kadamar da kwayoyin ga kwastomomin sa.

‘Yan Sandan sun kame Uzoma ne a yau da safe a Hauz Rani, kusa Malviya Nagar, wata masauka da ke a anguwar Rani, in da ya kan je don ya sayar da wannan muguwar kwayoyin (Cocaine) ga ma su saya.

“Mun karbi sanarwa ne da cewa Joseph Uzoma zai kawo mugun kwayoyin a nan Masaukar Hauz Rani” in ji fadin shugaban Jami’an tsaron.

“Wannan kwaya da muka kama Joseph da ita za ta kai kimanin kudi ‘Rs 20 lakh’ na kudin India idan an sayar da ita” in ji Vijay Kumar, DC na ‘Yan Sandan Jihar a bayanin sa da manema labarai na Dailyhunt Hindi a kasar India.

Naija News ta ruwaito da cewa Kwamitin Shugabanci da Manyan Sarakunan Arewacin Kasar Najeriya sun yi ganawa don magana akan dakatar da anfani da Miyagun Kwayoyi a kasar Najeriya.

“Bincike ya nuna da cewa daga cikin mugayen kwayoyi da ake amfani da ita a kasar Najeriya sune kamar taba, sigari, kaffin,  tramadol da codeine. kwamitin zata yi iyakar kokarin ta don taimakawa wadanda suka bar wannan halin”. in ji Dolapo a wata rahota da Naija News Hausa ta bayar ‘yan lokatai da suka wuce.

 

Karanta kumaZana’izar Tsohon Shugaba Shehu Shagari a Sokoto