Connect with us

Uncategorized

Ba tabbacin zabe ta gaskiya idan har Amina Zakari ce zata kula da harkan – PDP

 

‘Yan Jam’iyyar PDP sun yi kira da cewa ba su yarda da Amina Zakari ba a zaman Kwamishanan kulawa da kirgan zabe ta 2019.

“Kamar yadda kashi 90 na Jam’iyo’in siyasa ta Najeriya ba ta yarda da wannan ba, haka kuwa mu ma ba mu yadda da wannan ba” in ji Ologbondiyan, Magatakardan Jam’iyyar PDP ta Kasa.

Wannan mataki da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na sanya dangin sa ga matsayin kwamishanan kulawa da kirgan zaben 2019 ba gaskiya ba ne, wannan shiri ce na ganin cewa an yi makirci ga zaben, kuma renin wayo ne ga al’umman Najeriya gaba daya.

“Jam’iyyar mu na a sane da shirin makirci da Shugabancin Buhari ta yi wajen amfani da Amina Zakari da wadansu wajen makircin zaben da aka yi a Jihar Ekiti da Jihar Osun” in ji Ologbondiyan.

Ya kara da cewa “Muna bukatan kwamitin sulhu na Duniya da dukan al’umma su san da hakan cewa, idan har Amina Zakari ta saura a matsayin ta na Kwamishanan kulawa da kirgan zabe na Hukumar INEC, to lallai babu tabbacin samar da zabe ta gaskiya a Najeriya domin tana da daman yin makirci”.

Jam’iyyar ta ce da yawa cikin Jam’iyyar siyasa ta Najeriya sun nuna rashin amincewa da wannan nadin da hukumar INEC ta yi.

Naija News ta ruwaito da cewa Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) gargadi ‘yan jam’iyyar PDP da cewa su yi shiru da ƙoƙarin nuna iyawa da koya wa hukumar yada za ta kadamar da aikinta a ranar Alhamis da ta gabata.

An bayar da cewa bayan matsayin Amina Zakari a zaman Kwamishana na kulawa da kirgan zabe ta kasa, Mijin ta ma dan Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi.

“Amina Zakari ta kasance da halin makirci ganin irin yadda ta tafiyar da shirin zaben na yammacin kasar kwanakin baya da suka wuce, haka kazalika dangantakar ta da shugaba Muhammadu Buhari, ba mu yadda da wannan ba” in ji fadin wata Shugaban kungiyar Mata, Malama Esther Okpaluwah a birnin Abuja a ganuwan ta da manema labarai ranar Lahadi da ta gabata.

Karanta kuma Hukumar gudanar da zaben kasa ta Najeriya (INEC), ta karyace zargin da ‘yan Jam’iyyar PDP ta yi da cewar Hukumar na da shirin makirci ga zaben 2019 da ke gaba.

 

Advertisement
close button