Connect with us

Uncategorized

Mun kashe wani shugaban ‘Yan Fashi a Jihar Katsina – ‘Yan Sanda

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya a ranar 4 ga Watan Janairu, 2019 sun kashe wani da ake zargin sa a zaman shugaban ‘yan fashi a Jihar Katsina tun lokatai da dama.

Kane Mohammed, dan shekaru 35 da aka fi sanin sa da suna ‘Dan Mai-Keke’ da ake zargin sa da zaman dan fashi da kuma matsayin daya daga cikin shugaban ‘yan fashin Jihar Katsina, ya mutu a ranar Lahadi a yayin da ya yi wata ganuwa da Jami’an tsaron ‘Yan Sanda.

Naija News ta ruwaito da cewa Abdulmalik Umar, wani  shahararen shugaban Yan Boko Haram da ake zargin sa da alhakin mutuwar mutane fiye da 200 ya fada hannun yan sanda Najeriya a birnin Legas.

SP Gambo Isa, Mai yada labarun hukumar ‘yan sandan da ke a Jihar, a jiya Lahadi ya tabbatar da wannan ga manema labarai a Jihar Katsina.

“Wannan ya faru ne a ranar hudu 4, ga Watan Janairu, 2019 a tsohuwar kasuwa, wata mabuyar mugayen ‘yan fashi da ke a yankin Bakori na Jihar katsina a yayin da muke cikin faturo” in ji SP Isa.

Isa ya ce, ‘yan fashin sun haro ma rukunin faturo din mu ne da wasu mugayen makamai har ma sun yi wa daya daga cikin mu rauni, in ji shi.

An harbi shugaban ‘yan fashin harma ya mutu da baya a yayin da ake masa kulawa a asibitin da ke Bakori.

“Kane na daya daga cikin mugayen ‘yan fashi da ake bukatar kamawa da dadewa, zamu kuma ci gaba da bin cike har sai mun kai ga kame sauran ‘yan kungiyar”. in ji Isa.

 

Karanta kuma Shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, FPRO, Ag. DCP Jimoh MOSHOOD ya bada tabbacin cewa jami’an za su yi iya kokarin su da ganin cewa babu wata matsala ga Zaben 2019 da ke gaba.