Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari ya Sanya Rewane a matsayin Shugaban Kwamitin kadamar da Sabon Albashin Ma’aikata

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan tattaunawa da gwagwarmaya tsakanin Kungiyar Ma’aikata da Gwamnatin tarraya hade da wasu hukumomi da ke kasar, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya Mista Bismarck Rewane  wani babbaan jami’in gudanarwa na kudi a matsayin shugaban kwamiti na kadamar da hanyoyin da kuma tsarin yadda za a gudanar da sabon tsarin albashin ma’aikatan kasar.

Naija News Hausa ta ruwaito da baya da cewa Gwamnonin Jihohin Najeriya duka sun yi wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari don tattauna akan tsarin sabon albashin ma’aikata  

Ko da shike a taron da Gwamnonin suka yi kamin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnonin sun dage da cewa ba za su iya biyan kudi Naira dubu 30,000 ba, idan ko hakan ya tabbata lallai wasu ma’aikata za su rasa ofishin su.

Bayan kuwa Kungiyar ma’aikatar kasar sun yi barazanar cewa za su ci gaba da yajin aiki idan har gwamnatin tarraya ta yanke shawarar biyan ma’aikata kudi kasa da Naira dubu 30,000.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da cewa gwamnatin tarayya na da kulawa ta muhinmi ga wannan shiri na kadamar da sabon albashi ga ma’aikata. Ya fadi hakan ne a wajen ganawa da aka yi tare da Majalisar tarayya (FEC) a ranar Laraba 9, ga Watan Janairu, 2019 a birnin Abuja.

Ya ce, Kwamitin an kafa ta ne domin su yi zama su kuma tsarrafa hanyoyi da za a sami kudi don kadamar da wannan sabon albashi da ma’aikata, da kuma ganin cewa wannan shirin bai kawo raunanawa ba ga tattalin arzikin kasar da kuma sa ma’aikata rasa aikin su. in ji shi.

“Kasar na da isasshen kudi don aiwatar da wannan shiri na sabon albashi ga ma’aikata” in ji Shugaba Buhari.

 

Karanta kuma: Ba mu yarda da Amina Zakari ba a matsayin Kwamishanan kulawa da kirgan zabe ta 2019 – inji Jam’iyyar PDP