Uncategorized
Gamawa Babawo ya yi murabus da Jam’iyyar PDP, ya koma Jam’iyyar APC

Sanata Gamawa Babayo, Mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP ta Arewa da Jam’iyyar ta dakatar a ranar Litini da ta gabata ya koma wa Jam’iyyar APC.
A ranar Litini da ta gabata, rahoto ta bayar da cewa Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) sun dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyan arewa, watau Sanata Gamawa Babawo wanda su ka yi wa zargi da cewa sun same shi da halin munafunci da kadamar da ayuka da jam’iyyar ba ta amince da ita ba. Shugaban yada labarai ta Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya sanar da dakatarwar na sanata Babawo a ranar Litini 7, ga watan Janairu, 2019.
Kakakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mista Femi Adesina ne ya sanar da komawar Gamawa zuwa Jam’iyyar APC a ranar Talata da ta gabata a yayin da ya zuba hoton Gamawa da Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar tare da Hon. Kaulaha Aliyu a yanar gizon nishadin Facebook inda suka ziyarci gidan zamar shugaba Muhammadu Buhari a ranar 8 ga Watan Janairu, 2019.
Karanta kuma: Sanatan Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya mikar da kansa ga hannun Jam’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya.
Sami cikakun labarai da ga Naija News Hausa