Connect with us

Uncategorized

Miyetti Allah ta Jihar Taraba sun gabatar da Zabin su ga zaben 2019

 

Kungiyar zamantakewa da al’adun Fulani (Miyyeti Allah) ta jihar Taraba a ranar Litinin sun amince sun kuma gabtar da sabon zabin su ga dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Gwamna Darius Ishaku ga zabe ta gaba.

Naija News Hausa ta ruwaito da baya da cewa, Kungiyar Miyyeti Allah sun ce za mu bayyana zabin mu ga al’umma duka a kan kowaye za mu jefa wa kuri’ar mu ga zaben 2019 da ke a gaba bayan mun yi binbini da bincike ta gaske da ganin irin shiri da kowane dan takaran shugaban kasar ke da ita ga al’umma da kuma shirin da su ke da ita ga kungiyar mu.

Shugaban kungiyar na Arewa maso Gabas, watau Alhaji Mafindi Danburam ne ya jagoranci zamar amincewar da kungiyar ta yi da sanya Ishaku da Atiku a matsayin ‘yan takara biyu da zasu jefa wa kuri’ar su a zaben 2019, a yayin da suka yi zaman a fadar gwamnatin Jihar Jalingo.

Ya ce, wannan mataki ya kasance abu ne mafi kyau ga ‘yan uwa Fulani ta kasar.
Danburam,Shugaban kungiyar Fulanin ya ce, da farko dai bamu gane nufin Gwamnan Jihar ba, shi yasa bamu amince da matakin sa ba da ya gabatar da baya amma yanzu mun gane kuma mun amince da wannan kyakyawan shiri.

“Gwamnan ya yi alkawari da cewa zai kara tsarrafa wannan shirin, mun amince da wannan kuma muna shirye don mu ga kyakyawan shiri da ya ke da ita garemu a matsayin kungiya.

Karanta kuma: Asalin naman Kilishi da dandalin sa 

Advertisement
close button