Connect with us

Labaran Najeriya

Mun bada gaskiya gareka – Shugabanan Jihar Borno sun fada wa Muhammadu Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Manyan shugabanan Jihar Borno da Gwamnan Jihar sunyi wata Ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari

“Ya Shugaba” muna a nan ne matsayin mutanen da suka yi aiki, suka kuwa yi addu’a, kuma suka jira ga shugabancin ka, da bangaskiya mara matuka da cewa idan har ka na a shugabancin kasar, ta’addacin Boko Haram zai zo ga karshe tarihin Jihar Borno”.

Wannan shi ne fadin manyan shugabanan Jihar Borno da Gwamnan Jihar, Kashim Shettima, a wata ganuwa da suka yi a Aso Rock, a birnin Abuja don gabatar da bukatar su ga Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa don magance ayukan ta’addacin Boko Haram da sauran kashe-kashe da ke aukuwa a Jihar.
Ganawar ta kumshi Sanatocin Jihar guda Uku, ‘Yan Majalisar wakilai, Dan takarar Gwamna ta Jam’iyyar APC na Jihar da manyan Malaman addini da ta gargajiya.

Naija News ta ruwaito da cewa Matar Shugaban kasa Aisha Buhari ta gargadi Mata da Matasa don su goyawa mijinta baya ga zaben 2019

“Muna a nan ne don mun bada gaskiya da cewa za ka sauraremu kuma za ka nuna mana kulawa mafi mahimanci” in ji bayanin Shettima ga Shugaba Buhari.

“Gwamnan, Kashim Shettima ya zubar da hawaye a yayin da ya ke wannan bayanin”.

Ka nuna wa Jihar Borno kulawa ta gaskiya ta wurin yaki da ganin cewa ta’addanci tai kai ga karshe a Jihar, kuma tun shekara ta 2015 ka bamu isashen goyon baya da nuna kokari, “ba mu kuwa cire zato ba kuma ba mu saki kari ba” mun ba da gaskiya za ka mayar da zaman lafiya ga al’ummar Jihar mu.
“Kuma mun ba da gaskiya cewa Allah zai ba ka nasara ga shugabancin ka, kuma zai tabbatar mana da zamantakewa ta lafiya”.
Ya Shugaba, “Mun zo ne da bukatu da dama, da kuma wasu abin nazari guda goma da ke bukatar kulawa ta gagawa” in ji shugabannan.
Ko da shike basu bayyana wannan bukatu da nazirin bag a manema labarai. Amma dai nan gaba kadan za a bayyana shi ga jama’a duka watakila.

Karanta kuma: Jihar Katsina na cikin mawuyacin hali – inji Gwamna Masari