Connect with us

Uncategorized

Sabuwar Hari a yankin Kuje

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Asabar da ta gabata, a misalin karfe 11:47 na yamma, rahoto ta bayar da cewa wasu ‘yan hari sun kai farmaki ga kauyen Gudun Karya, da ke a yankin Kuje a inda suka harbe mutum uku da ke a shiyar bayan ganin cewa basu cin ma wanda suka ce nema ba.
“Lallai sun zo ne da yamma a ranar Asabar a missalin karfe goma sha biyu saura 11:47 (pm)” in ji wani mai suna Usman, mazaunin kauyen wanda ya ji, kuma ya ke da cikakken sani da harin.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Jami’an Sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘Yan Matan Boko Haram Uku a Jihar Borno

Usman yace, maharan su fado ne da yamma a kauyen kusan karfe shabiyu na dare, sun zo ne da bukatar su kame wani amma ba su cin masa ba. ganin hakan sai suka fara harbe-harbe ko ta ina har alsasun bindiga suka fada wa wasu, su ka kuwa ji rauni sosai da gaske.
kowa ya rikice a yayin da aka ji karar bindiga a sama. “Ni ma na fito ne bayar da suka wuce” in ji Usman.

Rahoto ba bayar cewa Ciyaman din yankin, Alhaji Abdullahi D. Galadima ya ziyarci wadannan da suka sami rauni a ranar Lahadi da ta gabata a wata asibitin da ke kauyen Lokogoma, bayan ya sami tabbacin wannan harin, daga bakin mai bada shawara da kuma mai yada labarai ga ciyaman din yankin, in ji Haruna Usman.

A yayin da wannan abin ya faru, an buga wa Shugaban ‘Yan Sanda DSP Anjuguri Manzah, wanda ke kulawa da ‘Yan Sandan yankin FCT waya, amma bai dauki wayan sa ba, kuma bai mayar da sakon da aka aika masa ba a wannan lokacin.

Karanta kuma: Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara ya kai ziyara ga sojojin da aka yiwa rauni a wani harin da wasu Mahara  suka yi kai masu a ranar Asabar da ta gabata.