Uncategorized
Fada ta barke tsakanin Egbira da Bassa a Jihar Kogi
Farmaki ya tashi tsakanin mazaunin Jihar Kogi biyu, watau yaren Egbira da Bassa-Kwomu.
Mataimakin shugaban Jami’an ‘Yan Sanda da ke a yankin, Mista Williams Aya ne ya bayyana wannan a garin Lokoja a yayin da yake gabatar da yadda fadan ta abku tsakanin yaruka biyun a ranar jiya nan Jihar Kogi.
Mista Williams ya ce, fadan tsakanin yaran Egbira da Bassa-Kwomu ya fara ne tun ‘yan watannai da dama sakamakon dawowar da Egbira suka yi zuwa wajen zamar su da aka kore su kwanakin baya da ya wuce.
Mun iya ganewa a Naija News cewa an ce yaran Egbira su dawo ne da zamantakewar su daga inda aka kore su shekarun baya da suka shige bayan gwagwarmaya da shawarwari daga bakin manyan yankin.
Anyi hakan ne don kadamar da zaman lafiya tsakanin mazaunan yankin duka.
Fadan ta barke ne jin irin maganar cin zuciya da sarkin Bassa-Gwomu ya yi wa yaran Egbira, da cewa su je garin Lokoja ko kuma inda daman suka zauna a lokacin da aka kore su da baya.
“Ku je can Lokoja ko kuma in da daman kuke kamin aka kira ku, ku tare can” in ji Sarki William Keke da ke jagoran yankin ‘yan Aguma na Bassa.
Wannan maganar ta sa ne ya barkar da fada.
Rahoto ta bayar da cewa Jami’an tsaro da ‘Yan takarar siyasa da ke a yankin sun je daman sun kai ga yarjejeniya don ganin cewa Egbira sun dawo wajen zaman su kamin aka kore su; Egbira na batun dawowar ne sai Williams Keke ya zubo masu da wannan kalmar bacin rai da har ya kai su ka fada har ma wasu sun rasa rayukan su, kuma wasu da yawa sun ji raunuka sosai.
Karanta kuma: Bayan kwanaki da dama Sanata Dino Melaye ya mikar da kansa ga Jami’an Tsaro da ke kewaye a gidansa.