Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a 11, ga Watan Janairu, a Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a 11 ga Watan Janairu, 2019

1. Gwamnonin Jam’iyyar APC ba su halarci taron gudanarwar shirin zaben Shugaban kasa ba

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun ki halartar taron baje kolin jam’iyyar APC da aka yi a ranar jiya a birnin Abuja.

A yayin da ake jiran Gwamnonin don su jagoranci jihar su, amma ba su halarci taron ba.

2. Na kashe fiye da Naira miliyan 200 daga asusu na akan yakin neman zabe – Moghalu

Kingsley Moghalu, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar YPP ya ce ya kashe kudi kimanin Naira miliyan 200 a kan shirinsa na cin zaben shugaban kasar Najeriya.

Ya bayyana cewa ba shi da uban siyasa kuma kudin kadamar da neman zaben shi zai fito ne daga tallafi daga hannun mambobinsa da masoyan sa.

3. Alƙali ya janye kansa ga shari’ar Gwamnar Adamawa na amfani da takadar karya

Alkalin da ke gudanar da karar amfani da takardar banza da Jibrilla Bindow Gwamnar Adamawa ya yi, Alkali Abdulaziz Anka ya ce ya janye kansa daga karar, da cewa bai kasance da kwanciyar hankali ba akan karar.

Alkali Anka ya sanar da janye kansa daga shari’ar a cewar bai kansance da kwanciyar hankali ba akan karar kuma zai mika karar ga babban alkalin kotun Tarayyar don sake mika karar ga wani alkali.

4. Boko Haram: Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikatan ta 260 da ke Jihar Borno

Saboda irin hare-haren da kungiyar Boko Haram ke aiwatar wa a Jihar Borno, kimanin ma’aikata 260 ne ‘yan Majalisar dinkin duniya suka janye ma’aikatan su daga kananan hukumomi uku a Jihar.

Samantha Newport, kakakin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Najeriya a jiya cikin wata sanarwa ta bayyana cewa hare-haren da kungiyar ta’addanci ke yi ya shafi aikin taimako da kungiyar ke yi wa yankin.

5. Shugaban ‘yan Jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya kalubalanci Tinubu gabatar da yadda ya tara dukiyarsa

Uche Secondus, Babban ciyaman na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa da ke a jihar Legas suna ikirarin yaki da cin hanci da rashawa bayan su ma da kansu sun tara arzikin su ne ta hanyar haka.

Ko da shi ke, Uche bai ambaci sunayen wadannan ba a yayin da yake jawabi a wata ganawar kamfen da suka yi a jihar Nasarawa a ranar Alhamis, ya ce wadannan ‘yan siyasar na kwanciya cikin kudin da suka sata amma sai ga shi suna na ikirarin yaki da cin hanci da rashawa.

6. Bamu bayyana amincewa da Atiku ba- in ji Ohanaeze

Kwamitin tsara al’adun gargajiyar Igbo, Ohanaeze Ndigbo sun yi watsi da zargin da ke yawo da ita da cewa sun bayyana amincewa da Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP.

Chuks Ibegbu, sakataren samar da labaran kungiyar ne ya bada wannan haske a wata ganawar manema labarai da aka yi a Jihar Enugu a ranar Alhamis da ta gabata.

7. Dalilin da yasa babu dan Kungiyar Ma’aikata (NLC) daya cikin Kwamitin tsarin albashi da Buhari  ya kafa

Shugaban Hukumar Ma’aikata na Najeriya (NLC), Ayuba Wabba ya bayyana dalilin da ya sa babu mutum daya daga kungiyar a cikin kwamitin fasaha na kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi.

Ayuba ya ce, Ministan Harkokin Kasuwanci da Harkokin Jakadancin, Dr. Chris Ngige ya rigaya a baya ya bayyana da cewa, “Gwamnatin tarayya ne ke da gudanarwa akan kowace shiri na kungiyar” cewa babu abin da ya kumshi Kungiyar NLC.

8. Mutane da yawa sun ji rauni a yayin da jirgin kasa ya yi hatsari a Jihar Legas

Rahoto ta bayar da cewa mutane da dama sun ji rauni sakamakon wani hatsarin jirgin kasa da ya faru a shiyar Kasuwar Ashade Ram, da ke Agege a Jihar Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya.

Jirgin ya fadi ne a  Mangoro/Agege a ranar Alhamis 10 ga watan 2019, a yayin ta kamo hanyar ta daga Ijoko, Jihar Ogun zuwa Ebute Metta, Jihar Legas.

9. Salon Tsarin Saraki na da karfi sosai, za ku gani – in ji Saraki

Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana yakin cin hanci da rashawa da shugaba Muhammadu Buhari ke yi a matsayin “Yakin farfaganda ne da ke nisa da ainihin gaskiyar”.

Saraki ya ce, ku jira za ku gani idan sakamako ya fito.

10. Sojojin Najeriya ta kai ga cin zarafin ‘yan Boko Haram a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa sun kai ga karfafa da kuma cin nasara ta gaske a yakin ta’addanci da hare-hare a Arewacin Kasar, a yayin da kwamandan Sojojin ya raunana karfin ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da ke yankin Zare, Kukawa, da kuma Kauwa da Gudumbal a Arewacin Jihar Borno.

Brig.-Gen. Sani Usman, kakakin yada yawun rundunar sojojin ne ya tabbatar da wannan ci gaba a wata sanarwa; ya ce rundunar sojojin ta samu cin nasara ne sakamakon goyon bayan Sojojin Sama da Sojojin Ruwa da suka hada hannu da su wajen yakin.

Samu cikakkun labarai da ga Naija News Hausa

Advertisement
close button