Connect with us

Uncategorized

Rundunar sojojin Najeriya sun ci nasara a yaki da Boko Haram a garin Baga da ke Jihar Borno

 

Rundunar Sojojin sunyi barazanar cin nasarar yaki da ‘yan Boko Harama a garin Baga da ke Jihar Borno

Rahoto ta bayar a baya da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye yankin kuma sun yi ta barazana da kuma kai farmaki ga yankin sojoji da ke a jihar a ranar 28 ga Watam Disamba a shekarar 2018 da ta gabata.

Amma an samu sabuwar tabbaci daga rahoton da Sani Usman, kakakin rundunar sojojin kasar ya rattaba hannu a ranar jiya da cewa sojojin sun sami cin nasara kan ‘yan ta’addan da ke a yankin Baga.

Sani ya ce “A gwagwarmayan cin nasara da ‘yan ta’addan da suka mamaye jihohin Islam ta Yammacin Africa (ISWAP), Rundunar sojojin Najeriya ta musamman (NASFC) da Operation LAFIYA DOLE sun hada hannu kuma sun yi wa ‘yan ta’addan Boko Haram cin mutunci na kwarai da gaske”.

Da safen nan Naija News ta sanar a layi na goma na Manyan Labaran Najeriya da cewa Sojojin Najeriya sun yi Ikirarin cin nasara da yan Boko Haram da ke yankin Zare, Kukawa, da kuma Kauwa da Gudumbal a Arewacin Jihar Borno.

“Ko da shi ke wasu daga cikin ‘yan ta’adda sun yi kokarin shiga sansani dakarun Monguno, amma sojojin dakarun sun yi mayar da hankalin su shiya daya suka kuwa hare su da harbi har ma sun kwato makamai da ke a garesu.

 

Karanta kuma:  Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai bada izi ni ba don ayi amfani da asusun kasar wajen gudanar da neman zaben 2019, ya ce ba za ni yi hakan ba kamar yadda gwamnatin da ta saba yi.

 

Advertisement
close button