Connect with us

Uncategorized

Sani, Jamilu da Abdu na fuskantar Shari’a a Kotun Jihar Katsina akan mungan laifuka da suka aikata

 

Kotun Jihar Katsina ta sa wasu mazaje uku gaba akan laifukan da ake zargin su da aikatawa

Abdullahi Sani da shakaru 35, da Jamilu Isah mai shekaru 25 da kuma Sani Abdu dan shekaru 25 na fuskantar shari’a a kotu don mungan laifukan da aka same su da ita a yankin Dusinma da ke Jihar Katsina.

Rahoto ta bayar da cewa mutanen kauyen ne suka kai karar Abdullahi, Sani da Jamilu ga ‘yan sanda ganin irin mugan halaye da laifukan da dama suke aiwatar a yankin tun da baya.

  • Jami’an ‘Yan Sanda sun bayar da cewa an kama Sani ne da laifin satan Babur da kuma halin kwace da sace-sace a nan yankin.
  • Isah kuma an kame shi ne da laifin satan awaki
  • Shi kuma Abdu an same shi ne da fashe-fashen shagunar mutane da gidaje

Naija News Hausa da baya ta ruwaito da cewa Gwamna Masari ya ce Jihar Katsina na cikin kangin ‘Yan Hari a wata gabatarwa da yayi a bikin ganawa a Jihar Katsina da Jami’an tsaron Jihar duka.

“Jiharmu a halin yanzu tana cikin mawuyacin hali da irin hari da sace-sacen mutane da ake yi, Idan har suka kame mutum, sai su bukaci kudi kuma idan har ba a samu biyar kudin ba, sai su kashe wannan da ke a kame”. in ji Masari.

Bayan da ‘Yan Sanda suka yi binciken su, sun gane da cewa ba lallai zargin da ake yi da su ukun gaskiya ne kuma babu mai bayani ta kwarai ko wata maganar mafita cikin su ukun.

An kuma bayar da cewa Abdu ne kawai ke a kotu a daidai lokacin da aka kafa baki ga lamarin su a ranar jiya Alhamis 10, ga watan Janairu, 2019.

 

Karanta kuma:  Manyan shugabanan Jihar Borno da Gwamnan Jihar sunyi wata Ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a wata ganuwa da suka yi a Aso Rock, a birnin Abuja.

Advertisement
close button